Aiki daga Landan: Shugaba Buhari ya rattaba hannu dokar harajin hakar danyen man cikin ruwa

Aiki daga Landan: Shugaba Buhari ya rattaba hannu dokar harajin hakar danyen man cikin ruwa

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya rattaba hannu da gyararren dokar harajin hakar danyen man fetur dake cikin rafi a ranar 4 ga Nuwamba, 2019.

Sabanin yadda aka saba ganinsa yana rattaba hannu a fadar shugaban kasa, Buhari ya sanya hannun ne a gidan gwamnati dake birnin Landan inda ya yada zango daga Saudiyya domin hutawa.

A cewar Malam Garba Shehu, shugaba Buhari ya bayyana cewa wannan gyara babbar nasarace ga Najeriya a yau.

Yace: " Yau rana ce mai muhimmanci ga dukkan yan Najeriya - musamman masu kananan shekaru."

"A yau na rattaba hannun da gyararriyar dokar hakar man fetur cikin ruwa. A yanzu Najeriya za ta rika samun nata rabon da take da hakki da shi na arzikin kasarmu karo na farko tun shekarar 2003."

"A dukkan shekarun da suka shude Najeriya ta yi kasa a gwiwa wajen amsan nata rabon na man da aka haka, saboda duk yunkurin da akayi na gyara dokar bai yiwu ba. Sai yau.

"Hadin bakin yan siyasan Najeriya da kuma kamfanonin mai na tsawon sama shekaru 25 wajen barin kudin harajin danyen mai a $20 ga kowace ganga duk da cewa farashi ya ninka haka sau uku."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel