Johnson Suleman: Duk da Sowore ya bata mani rai, zan iya tsaya masa a kotu

Johnson Suleman: Duk da Sowore ya bata mani rai, zan iya tsaya masa a kotu

Babban malamin addinin kiristan nan, Apostle Johnson Suleman, ya yi magana game da halin da ‘dan takarar shugaban kasa kuma Jagoran #RevolutionNow, Omoyele Sowore, ya ke ciki a yanzu.

Fasto Apostle Johnson Suleman na cocin Omega Fire Ministries na Duniya, ya fara nuna yiwuwar ya tafi kotu ya tsayawa Omoyele Sowore wajen ganin an bada belinsa da ya ke nema ya gagara.

Mun fahimci cewa babban Limamin na cocin Omega Fire ya yi amfani da shafinsa na sada zumunta na Tuwita a Ranar Litinin dinnan, 4 ga Watan Nuwamba, 2019, ne ya yi wannan magana.

Malamin addinin ya tado maganar Omoyele Sowore ne da kimanin karfe 10:00 na safe inda wasu Mabiyansa su ka taya sa tofa albarkacin bakinsu. Wasu sun nemi Malamin ya zare hannunsa.

KU KARANTA: Gabon ta tuba wurin Allah bayan wani babban kuskure

A irin wannan yanayi, me Yesu zai yi? Suleiman ya jefa tambaya. Limamin Kiristan ya cigaba da cewa: “Ina tunanin tsayawa domin a bada belinsa. Malamin ya fada a ainihin shafinsa na Tuwita.

"Na damu ganin cewa babu wanda zai tsayawa @YeleSowore. Eh babu shakka ya kuntatawa jama’a, har da ni a cikinsu. Amma za mu maida hankali ne a kan wannan mu kyale shi ya bushe?”

Malamin mai Mabiya a fadin kasar nan ya ke tambaya cewa ko da sabon shiga siyasar shi ya jawowa kansa halin da yake ciki, me Yesu zai yi idan Bawa zai burma cikin irin wannan yanayi.

Watanni uku kenan ana tsare da Yele Sowore a Najeriya tun bayan da hukumar DSS ta kama shi a cikin Watan Agustan 2019. Gwamnatin tarayya ta na tuhumar Sowore da laifin cin amanar kasa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng News

Online view pixel