Majalisar Tarayya sun fara kokawa game da gabatar da kasafin kudin badi

Majalisar Tarayya sun fara kokawa game da gabatar da kasafin kudin badi

Mun ji cewa majalisar wakilan tarayya ta fara bayyana cewa kare kundin kasafin shekara mai zuwa da ake yi a gabanta ya na daukan fiye da lokacin da ta shirya saboda wasu dalilai.

Daga cikin dalilan da su ke jawo bacin lokaci wajen aikin kasafin kudin a majalisa akwai rashin gabatar da kasafin hukumomi da ma’aikatun gwamnati da shugabanninsu su ke yi da kyau.

Majalisar wakilan ta yi Allah-wadai da irin aikin da wasu hukumomi da ma’aikatu na gwamnatin tarayya su ke yi. Dole ta sa aka rika kora wasu MDA domin su je su yi wa kasafinsu kwaskwarima.

Mai magana da yawun majalisar wakilan na Najeriya, Honarabul Benjamin Kalu, ya bayyana wannan a wata tattaunawa da ya yi da Daily Trust kamar yadda mu ka ji a Ranar 4 ga Nuwamba.

Benjamin Kalu, ya ke cewa: “Ya kamata ace an karkare kare kasafin kudi a majalisa. Mu na so mu kammala komai a Ranar 5 ga Nuwamba. Kun ga cewa mu na ta faman tsere ne da lokaci.”

KU KARANTA: NDDC: An kasa ya tsare a kan binciken ke-ke-da-ke-ke a Neja Delta

“Ya kamata ace mu auna kokarinmu. Mu dakata kadan sai mu duba abin da mu ka yi.” Inji Kalu. Sai dai ba haka ya kasance ba domin kuwa yanzu lokacin da aka dauka ya na gab da kurewa.

Duk da haka, Honarabul Kalu ya ce an ci nasara wajen wannan babban aiki da ake yi. Kalu ya ce ma’aikatu da hukumomi ba su ba majalisa kunya ba sai dai kurum ‘yan matsaloli da aka samu.

Bayan wannan kuma, Mai magana a madadin ‘yan majalisar wakilan ya ce shugaban kasa ya yi alkawari sakin 40% na kudin yin ayyuka a bana domin ba a son ware wasu sababbin kudi a 2020.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel