Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya ta gindaya sharudan bude iyakokin Najeriya

Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya ta gindaya sharudan bude iyakokin Najeriya

Gwamnatin tarayya ta gindaya wasu sharuda da tace ya zama dole a bi idan har za ta sake bude iyakokin kasar.

Ta ce lallai ya zama dole kasashen ECOWAS su mutunta dokar asali, inda ta sha alwashin cewa Najeriya ba za ta sake lamuntan sauya ainahin jakar kayayyakin da aka shigo da su daga waje ba.

Ta bayyana cewa duk wani kaya da zai shigo cikin kasa daga wata kasa da ke zaman mamba a ECOWAS dole ya kasance an sarrafa shi daga kayan cikin kasar ko ya kasance ya kunshi kaso 30% na kayan cikin kasar.

Ta jaddada cewa idan har za a shigo da kayayyaki kasuwar Najeriya daga wata kasa toh ya zama dole kasar ta yi wa kayan rakiya kai tsaye har zuwa boda.

KU KARANTA KUMA: Labari mai dadi: Kwanan nan shinkafa za ta yi arha ta yadda ba za ta fi karfin talaka ba – Gwamna Bagudu

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da kara tsayin wa'adin atisayen da aka yi wa lakabi da 'Exercise Swift Response' wanda ya jawo aka rufe iyakokin Najeriya na kasa da makwabatan kasashe.

An rufe iyakokin Najeriya ne tun ranar 20 ga watan Agusta, kuma ana saka ran bude iyakokin a ranar 31 ga watan Janairu, sabanin tsammanin da wasu ke yi na cewa za a bude iyakokin kafin lokacin bikin Kirsimeti domin 'yan kasuwa a yankin kasashen Afrika ta yamma su samu su sarara.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel