Kaduna: El-Rufai ya bayar da umarnin a biya sabbin ma'aikata dukkan bashin da suke bin gwamnati

Kaduna: El-Rufai ya bayar da umarnin a biya sabbin ma'aikata dukkan bashin da suke bin gwamnati

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai, ya bada umarnin biyan kusan malaman firamare 8,500 daga cikin 39,000 da gwamnatin jihar ta dauka aiki, basussukansu cikin satin nan.

A takardar da mai bawa gwamnan shawara na musamman akan yada labarai, Muyiwa Adekeye, ya fitar a ranar Asabar, gwamnan ya nuna rashin jin dadinsa a kan yadda kananan hukumomin suka rikewa malaman makarantar hakkokinsu.

Hakan kuwa ya faru ne da sabbin malaman makarantar firamare da aka dauka a rukuni na biyu a jihar.

"Bayan bayani daga ma'aikatar kanananan hukumomi da SUBEB, gwamnatin jihar ta gano cewa kananan hukumomi suna rike da kusan naira miliyan 1.8 na albashin malaman makarantar da aka dauka a karo na biyu. Albashin ya hada daga na watan Janairu zuwa Mayu 2019," in ji takardar.

Gwamnan El-Rufa'i ne gwamna na farko da ya fara biyan ma'aikatan jiharsa sabon karin albashin da shugaba Buhari ya saka wa hannu bayan samun sahalewar majalisun kasa.

Wata majiya ta bayyana cewa El-Rufa'i bai biya sabon karin albashin kamar yadda yake a cikin sabuwar dokar ba.

DUBA WANNAN: PDP ta garzaya kotu bayan da ta sha mugun kaye a zaben jihar Kebbi

Sai dai, sauran gwamnoni sun bayyana cewa zasu biya sabon karin albashin ne daidai da karfinsu, watau ba lallai ya kasance N30,000 zasu biya ma'aikatan jihohinsu ba a matsayin mafi karancin albashi ba.

Tuni kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta bayyana rashin amincewarta da wannan mataki da gwamnonin suka dauka, inda suka bayyana cewa duk gwamnan da ya gaza biyan mafi karancin albashin kamar yadda doka ta amince, zai fuskanci yajin aiki a jiharsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel