Fusatattun matasa sun kona barayin wayar salula 2 kurmus a jahar Delta

Fusatattun matasa sun kona barayin wayar salula 2 kurmus a jahar Delta

Wasu fusatattun mutane sun banka ma wasu matasa biyu da suke zargi da satar wayoyin salula a unguwar Ovwian, kusa da kwalejin sakandari ta Ovwian cikin karamar hukumar Udu dake jahar Delta, inji rahoton jaridar Punch.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mutanen unguwar sun zargi matasan biyu da laifin satar wayoyin wata mata da makudan kudade da misalin karfe 1 na rana a kan titin Ovwian, nan da matar ta kwantsama ihu, wanda ya janyo hankulan jama’a.

KU KARANTA: Hadimin Buhari: Obono-Obla ya tafka manyan laifuka guda 50 – Inji Minista Malami

Cikin dan lokaci kalilan jama’a suka raka barayin a guje har sai da suka cimmasu, sa’annan suka kamasu, inda ba tare da bata lokaci ba suka yi musu dukan kawo wuka, sa’annan suka warwatsa musu fetir, daga nan kuma suka banka musu wuta, nan suka kyalesu suka kone kurmus.

Wani shaidan gani da ido mai suna Adiza Jacob yace: “Mutanen biyu sun yi ma matar fashin wayanta ne da misalin karfe 1 na rana a ranar Lahadi, 3 ga watan Nuwamba, ihunta ya sa jama’a suka fahimci halin da take ciki, suka kai mata dauki.”

Shi ma wani mazaunin unguwar yace duk da dai cewa mutane sun dauki mummunar hukunci a kan matasan, amma yana fata hakan ya zamto izina ga sauran mutanen dake sha’awar yin sata, fashi da makami da sauran miyagun laifuka.

A wani labari kuma, jami’an runduna ta 81 na rundunar Sojojin kasa ta Najeriya sun samu nasarar cafke wasu gagga gaggan mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram yayin da suke tsaka da kitsa yadda zasu kaddamar da wasu hare hare a jahar Leags.

Rundunar Sojan ce ta sanar da haka a ranar Lahadi, 3 ga watan Nuwamba ta bakin babban kwamandan rundunar, Manjo Janar Olu Irefin, wanda yace tuni sun garzaya da yan ta’addan zuwa babbar birnin tarayya Abuja.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel