Hadimin Buhari: Obono-Obla ya tafka manyan laifuka guda 50 – Inji Minista Malami

Hadimin Buhari: Obono-Obla ya tafka manyan laifuka guda 50 – Inji Minista Malami

Ministan sharia’a, Abubakar Malami ya zargi tsohon hadimin shugaban kasa kuma shugaban kwamitin kwato dukiyoyin gwamnati da aka sace, Okoi Obono-Obla da gudanar da wasu haramtattun bincike masu yawa a yayin da yake ofis.

Jaridar The Nation ta ruwaito Malami ya bayyana haka ne cikin rahoton daya aika ma mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, inda yace a hukumance, bincike biyu kadai aka baiwa Obla daman bincikawa, amma ya yi gaban kansa ya gudanar da bincike guda 50!

KU KARANTA: Yadda muka kama barawon dake amfani da asusun banki 51 – Ibrahim Magu

A watan Nuwamba ne gwamnatin Buhari ta tsige Obla daga mukaminsa, sa’annan ta nemi ya mika kansa ga hukumar yaki da rashawa da makamanta laifuka, ICPC, amma sai Obla ya cika wandonsa da iska, ya ranta ana kare.

“Sanannen abu ne cewa kwamiyin SPIP bata da daman shigar da kowa gaban kotu, amma Obla ya dauki hayar lauyoyi su shirta takardun tuhume tuhume da zai mika ma kotu ba tare da neman izinin babban lauyan gwamnatin Najeriya ba.

“Daga cikin irin wannan har da binciken daya kaddamar a kan wasu Alkalai, inda ya nemi su bayyana kadarorinsu, wanda tuni Alkalan suka yi a gaban hukumar dake da hurumin bukatar hakan, hukumar da’ar ma’aikata.

“Wannan katobara ce ma tasa mataimakin shugaban kasa ya dakatar da Obla daga mukaminsa a shekarar 2017, ni kuma da haka na nemi Alkalan su janye wadannan bayanai da suka fitar, da wannan kadai sai a yi zaton bangaren zartarwa na kokarin danne bangaren sharia ne.” Inji Malami.

Sai dai a nasa bangaren, Obla ya aika ma shugaba Buhari wata budaddiyar takarda inda ya bayyana masa cewa bita da kulli Osinbajo ke masa saboda yana biyayya ga Buharin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel