Kungiyar kasashen Afirka ta karrama Magu a matsayin ‘Gwarzon yaki da rashawa’ na Afirka

Kungiyar kasashen Afirka ta karrama Magu a matsayin ‘Gwarzon yaki da rashawa’ na Afirka

Cibiyar yaki da rashawa ta kungiyar kasashen Afirka, (AU-ECOSOCC) ta karrama shugaban EFCC, Ibrahim Magu a matsayin gwarzon yaki da rashawa a nahiyar Afirka gaba daya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito kungiyar ta sanar da karrama Magu da lambar yabo na ‘Jagoran yaki da rashawa na musaman a Afirka’ a cikin wata sanarwa data fitar a ranar Litinin, 4 ga watan Nuwambar shekarar 2019.

KU KARANTA: Yadda muka kama barawon dake amfani da asusun banki 51 – Ibrahim Magu

Wakilin Najeriya a majalisar AU-ECOSOCC, Dakta Tunji John Asaolu ne ya bayyana haka, inda yace za’a karrama Magu ne saboda kwazo, kwarewa da kuma kokarin da yake nunawa wajen yaki da rasahwa a Najeriya, idan za’a tuna, AU ta nada Buhari a matsayin garkuwan yaki da rashawa na Afirka a shekarar 2018.

Dakta Tunji yace: “Muna sa ran wannan karramawa da za’a yi ma Magu za ta karfafa yaki da rashawan da shugaban kasa Muhammadu Buhari yake yi a Najeriya.” Inji shi.

Mista Tunji yace za’a gudanar da bikin karramawar ne a dakin taro na Ladi Kwali dake Otal din Sheraton a babban birnin tarayya Abuja da misalin karfe 6 na yammacin Talata, 5 ga watan Nuwamba.

A wani labari kuma, mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya bayyana cewa sun kaddamar da cikakken bincike a kan kasurgumin barawon nan Ismaila Mustapha wanda ya shahara wajen damfara da satar kudi ta yanar gizo.

Magu ya bayyana cewa Ismail Mustapha wanda ake kira da suna Momph ya saci makudan kudade da suka kai naira biliyan 14 ta kamfaninsa mai suna Imalob Global Investment Limited, sa’annan yana amfani da asusun ajiyan kudi na banki guda 51.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel