Da duminsa: Ganduje ya sake zaban kwamishanoni 20 (Jerin sunaye)

Da duminsa: Ganduje ya sake zaban kwamishanoni 20 (Jerin sunaye)

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya aika sunayen kwamishanonin da ya zaba majalisar dokokin jihar domin tantancesu da tabbatar da su.

Hadimin Ganduje kan yada labarai, Salihu Tanko Yakassai, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki inda yace:

"Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya aika da sunayen mutum 20 zuwa majalisar dokoki ta jiha domin tantance su da tabbatar da su a matsayin Kwamishinoni kuma yan majalisar zartarwa na Jihar Kano.

Kakakin Majalisa ne ya zaiyana sunayen a zaman majalisar da Safiya nan kuma ana sa ran fara tantancewar nan bada jimawa ba."

Ga jerin sunayensu:

1- Murtala Sule Garo

2- Engr. Muazu Magaji

3- Barrister Ibrahim Muktar

4- Musa Iliyasu Kwankwaso

5- Dr. Kabiru Ibrahim Getso

6- Mohammed Garba

7- Nura Mohammed Dakadai

8- Shehu Na’Allah kura

9- Dr. Mohammed Tahir

10- Dr. Zahara’u Umar

11- Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa

12- Sadiq Aminu Wali

13- Mohammed Bappa Takai

14- Kabiru Ado Lakwaya

15- Dr. Mariya Mahmoud Bunkure

16- Ibrahim Ahmed Karaye

17- Muktar Ishaq Yakasai

18- Mahmoud Muhammad

19 Muhammad Sunusi Saidu

20- Barrister Lawan Abdullahi musa

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel