Wata sabuwa: Hukumar kwastam ta ce babu ranar bude iyakokin Najeriya

Wata sabuwa: Hukumar kwastam ta ce babu ranar bude iyakokin Najeriya

Hukumar hana fasa kauri na Najeriya wato Kwastam ta bayyana cewa ranar 1 ga watan Janairu, 2020, da ke kunshe a wata takarda da aka fitar ba shine ranar bude iyakokin kasar da aka kulle ba.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar kwastam, Mista Joseph Attah, ne ya tabbatar da hakan ga majiyarmu ta Punch a wata hira ta wayar tarho a ranar Lahadi, 3 ga watan Nuwamba.

Attah yace ranar 31 ga watan Janairun, 2020 za ta kasance ranar kawo karshen rukunin farko na aikin da ake aiwatarwa, amma ba wai ranar kawo karshen rufe iyakokin ba.

Ya ce iyakokin za su cigaba da kasancewa a rufe a illa-mashaa-Allah har sai an cimma manufar da ya sa gwamnati ta rufe su.

Attah ya kara da cewa jami’an tsaro da ke filin aiki za su sanar da cigaban lamarin game da rukuni na biyu na rufe iyakokin kafin rana 31 ga watan Janairu.

KU KARANTA KUMA: Motar kamfen din dan takarar gwamna na PDP a Kogi ya kashe mutane 4

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da kara tsayin wa'adin atisayen da aka yi wa lakabi da 'Exercise Swift Response' wanda ya jawo aka rufe iyakokin Najeriya na kasa da makwabatan kasashe.

An rufe iyakokin Najeriya ne tun ranar 20 ga watan Agusta, kuma ana saka ran bude iyakokin a ranar 31 ga watan Janairu, sabanin tsammanin da wasu ke yi na cewa za a bude iyakokin kafin lokacin bikin Kirsimeti domin 'yan kasuwa a yankin kasashen Afrika ta yamma su samu su sarara.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel