Motar kamfen din dan takarar gwamna na PDP a Kogi ta kashe mutane 4

Motar kamfen din dan takarar gwamna na PDP a Kogi ta kashe mutane 4

Wata motar kamfen din jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) kirar G-Wagon a ranar Asabar ta yi karo da wani kwantenan kasuwanci inda ta kasha mutane hudu dake zama a wajen a yankin Idah dake jihar Kogi.

An tattaro cewa lamarin ya afku ne a Idah hedkwatar masarautar Igala.

An kawo cewa motar G-Wagon din ta kasance na dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP, Injiniya Musa Wada.

Wani babban jami’in karamar hukumar Idah, Cif Hilary Edime Amodu, ya nuna bacin ransa akan tukin ganganci da direbobi a lokacin kamfen.

A wani jawabi da ya saki a daren ranar Asabar Idachaba Muhammed, hadimin jigon ya bayyana cewa hatsarin ya afku ne a ranar Asabar da rana.

Sai dai an tattaro cewa har yanzu direban G-wagon din da mutanen da ke ciki suna cikin mawuacin hali a wani asibiti da ba a bayyana ba.

Wani idon shaida da ya nemi a boye sunansa yace jami’an tsaro na hadin gwiwa ne suka hana a far ma direban G-Wagon din.

KU KARANTA KUMA: Zaben gwamnan Bayelsa: Matasan PDP sun koka kan zargin daukar yan bindiga aiki

Sai dai kuma, sakataren labarai na kungiyar kamfen din Musa Wada/ Ardo, Faruk Asejoh wanda ya tabbatar da lamarin yace mutane biyu ne suka mutu yayinda mutum daya ya ji mummunan rauni kuma cewa yana asibiti.

Sai dai kuma duk kokari da aka yi domin jin tab akin yan sanda bai samu ba a lokacin wannan rahoton.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel