Zaben gwamnan Bayelsa: Matasan PDP sun zargi APC da kwasan yan jagaliya

Zaben gwamnan Bayelsa: Matasan PDP sun zargi APC da kwasan yan jagaliya

Gabannin zaben gwamnan jihar Bayelsa wanda aka shirya gudanarwa a ranar 16 ga watan Nuwamba, matasan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun yi zargin cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na diban makiyaya domin haddasa rigima da kuma magudin zabe ta yadda su za su yi nasara.

Da suke nuna damuwa kan lamarin, matasan na PDP karkashin inuwar ‘PDP South-south Youth Vanguard’ sun zargi APC da rashin goyon bayan gwagwarmayar Ijaw, amma sun shawarci jam’iyyar da ta janye daga duk wani launi na rikici a lokacin zabe.

Matasan, a wani jawabi daga shugabansu na kasa, James Efe Akpofure, sun yi zargin cewa abunda APC ke muradi kawai shine man fetur a dake jihar Bayelsa, cewa jam’iyyar bata da ra’ayi a cigaban jihar.

Matasan na PDP sun bayyana cewa a koda yaushe APC na neman hanyar mallakar akalla jiha guda daga yankin mai albarkatun man fetur, inda suka yi zargin cewa wannan ne dalilin da yasa jam’iyyar ta tayar da fitina a lokacin zaben gwamnan jihar Rivers.

KU KARANTA KUMA: Wasu Jami’an Gwamnati su na tsoron a binciki Hukumar NDDC - Akpabio

Matasan sun cigaba da bayyana cewa mutanen Bayelsa sun kasance wayayyu kuma cewa za su dakile duk wani ynkuri na APC a duk yanayin da ya zo.

Kungiyar matasan, tace a shirye take ta fuskanci yan bindiga, makiyaya ko kuma duk wani bata gari da APC ta dauka don zaben.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel