Wasu Jami’an Gwamnati su na tsoron a binciki Hukumar NDDC - Akpabio

Wasu Jami’an Gwamnati su na tsoron a binciki Hukumar NDDC - Akpabio

Ministan harkokin Neja-Delta, Godswill Akpabio, ya ce tsoro ya kama wasu jami’an gwamnati saboda binciken da ake shirin yi a hukumar NDDC mai kula da cigaban yankin na Neja-Delta.

Sanata Godswill Akpabio ya ce a matsayinsa na shugaba, a shirye ya ke da ya canza abin da ake fada game da hukumar NDDC don haka ya tabbatar wajen ganin an yi gaskiya a aikin hukumar.

Ministan da yake wani jawabi a Garin Abuja, ya jaddada aniyarsa na gyarawa hukumar NDDC zama domin habaka yankin kasar ta hanyar jawo masu zuba hannun jari daga kasashen Duniya.

Godswill Akpabio ya yi wannan jawabi ne a gaban wasu tubabbun Tsagerun yankin da su ka fito daga jihohin Akwa-Ibom da Kuros-Ribas yayin da su ka kai masa ziyara a karshen makon nan.

KU KARANTA: Buhari ya keta Landan bayan kammala aikin Umrah

A jawabin da Ma’aikatar Neja-Deltan ta fitar Ranar Lahadi, 3 ga Watan Nuwamba, Mai girma Ministan yace jama’an Gari za su fi more rayuwarsu idan aka yi wa hukumar NDDC garambawul.

Akpabio ya ce babu wani surutun na wadanda su ka ci karensu babu babbaka a hukumar ta NDDC a shekarun baya da zai sa ya fasa aikin da ya dauko na gyara yankin Neja-Delta mai arzikin mai.

Tsohon gwamnan na Akwa Ibom ya ce an narkawa NDDC makudan kudi a cikin shekarun baya, amma babu wani abin kirkin da za a iya gani don haka gwamnatin Buhari ta nemi ayi bincike.

Jawabin ya nuna za a taso ‘yan kwangilar da aka biya kudi amma su ka noke da su dawo da dukiyar gwamnati ko su je su yi aikin da aka ba su, tare da yabawa wasu da su ka yi wannan.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel