Yaki da ta’addanci: Sojoji sun kama mayakan Boko Haram guda 8 a Legas

Yaki da ta’addanci: Sojoji sun kama mayakan Boko Haram guda 8 a Legas

Jami’an runduna ta 81 na rundunar Sojojin kasa ta Najeriya sun samu nasarar cafke wasu gagga gaggan mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram yayin da suke tsaka da kitsa yadda zasu kaddamar da wasu hare hare a jahar Leags.

Jaridar The Nation ta ruwaito rundunar Sojan ce ta sanar da haka a ranar Lahadi, 3 ga watan Nuwamba ta bakin babban kwamandan rundunar, Manjo Janar Olu Irefin, wanda yace tuni sun garzaya da yan ta’addan zuwa babbar birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Zuwa daya: Jami’an EFCC sun nade shuwagabannin kananan hukumomi 16 a jahar Kwara

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan ta’addan sun yi kokarin kaddamar da hare hare ne a wata jami’a dake garin Legas a makonni biyu da suka gabata, amma aka yi sa’a Sojoji suka dakile yunkurin yan ta’addan, inda ta kama mutane 4 dake da hannu cikin shirin, sa’annan aka kama sauran daga bisani, dukkaninsu sun tabbatar da kasancewa a kungiyar Boko Haram.

A jawabinsa, Manjo Janar Olu Irefin yace: “Mun fara aikinmu ta karkashin kasa, kuma muna aiki tare da dukkanin hukumomin tsaro. Don haka kada jama’a su samu wata damuwa game da tsaro, a tsaye muke kyam don tabbatar da tsaron jama’a da dukiyoyinsu a jahar Legas.”

Shi ma kwamishinan Yansandan jahar Legas, Zubairu Muazu ya tabbatar ma al’ummar Legas cewa kada su samu wata fargaba game da tsaro a jahar, inda yace: “Legas na cikin aminci, akwai tsaro a Legas, babu wata barazanar harin Boko Haram, kuma kada jama’a su tsorata, bama barci a kan wannan lamari."

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel