Khadimul Islam: Ganduje ya kaddamar da shirin taimakon makarantun allo da islamiyya a Kano

Khadimul Islam: Ganduje ya kaddamar da shirin taimakon makarantun allo da islamiyya a Kano

A ranar Lahadi ne Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya kaddamar da cibiyar tallafin makarantun allo da islamiyya a jihar.

Ya ce, tallafin na daga cikin tsarin karatun firamare da sakandire a kyauta kuma dole a jihar, wanda aka kirkiro don rage yawan yaran da basa zuwa makarantar boko a jihar.

"Da tsananin godiya ga ubangiji nake kaddamar da gidauniyar tallafin makarantun allo da islamiyyu ta hanyar bada kayan abinci da kuma kudi ga Alarammomi 1,000 daga tsangaya 1,000 a fadin kananan hukumomi 44 na jihar Kano."

Ganduje ya jinjinawa kokarin abokan hadin guiwar gwamnati irinsu DFID, bankin duniya da kuma UNICEF.

Gwamnan ya jinjinawa UNICEF bisa tallafin da take bayar wa wajen habaka makarantun allon da islamiyyu da tayi da naira miliyan 105.

Kamar yadda yace, "mika chek din kudi na naira dubu dari biyu daga UNICEF ga makarantu 10 daga cikin makarantun allon 440 a jihar abin yabawa ne."

Yace, gwamnatin jihar ta kaddamar da shirin tallafawa makarantun allon da islamiyyun jihar ne ta hanyar samar da malaman darussan turanci da lissafi.

DUBA WANNAN: Wata mata ta shake 'ya'yan cikinta 2 har lahira bayan sun ki cin abincin da ta zuba wa guba

Ganduje yayi alkawarin daukar nauyin malaman makarantun allon da islamiyyun wajen karo ilimi a kasashe irinsu Saudi Arabia ta yadda zasu zamo malaman zamani da zasu samo sabbin dabarun koyarwa don karuwar dalibansu.

A jawabinsa, jami'in UNICEF, Maulid Warfa, yace UNICEF ta raba tallafin ga makarantu 300 da makaranttun allo 420 a fadin jihar Kano.

Ya bayyana cewa, UNICEF zata dubi makarantun da suka yi amfani da kudaden da aka basu ta yadda ya dace domin cin moriyar shirin a gaba idan wani tallafin ya samu.

Ya kara da cewa, kudaden tallafin sun fito ne da taimakon gwamnatin Kano domin tabbatar da tsarin karatu kyauta kuma na dole a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel