Watakila PDP ta sake ba Arewa maso Gabas/Kudu maso Gabas tuta a zabe mai zuwa

Watakila PDP ta sake ba Arewa maso Gabas/Kudu maso Gabas tuta a zabe mai zuwa

- Gwamnonin da ke wa’adin karshe su na kokarin samun iko a Jam’iyya

- Wike ya na nan a kan bakansa na ganin Aminu Tambuwal ya kai labari

- PDP ta ce babu maganar zaben shugaban kasa a kan teburinta tukuna

Mu na cigaba da samun labari cewa jam’iyyar PDP ta fara shirye-shirye a karkashin kasa na ganin yadda za ta dumfari 2023 bayan da ta sha kashi a shari’ar zaben 2019 a gaban koli.

Jaridar This Day ta rahoto cewa PDP ta na tunanin mika tikitin shugaban kasa zuwa yankin Arewa maso Gabas da Kudu maso Gabas kamar yadda ta yi a takarar Atiku Abubakar/Peter Obi.

A cikin karshen makon nan ne wasu Jiga-jigan PDP su ka fara kawo maganar yadda za a fito da ‘yan takara a zabe mai zuwa. Arewa maso Gabas da Kudu maso Gabas ne ba su taba mulki ba.

Bayan rashin mulkin wadannan shiyyoyi, ana tunanin APC mai mulki za ta kai tikitinta Kudu maso Yamma ko kuma Arewa maso Gabas ne a zaben 2023, don haka PDP ta fara na ta tanadin.

Wani babban Jigon PDP ya shaidawa This Day cewa kawo yanzu ba su fitar da matsaya ba tukuna, amma nan da ba dadewa ba jam’iyyar za ta fitar da jawabi a kan wannan tsari da ake sa rai.

“Mu na sane cewa shugaba Muhammadu Buhari ba zai yi takara a zaben 2023 ba, kuma rashinsa zai bar wani rami a cikin APC, don haka za mu yi kokarin hana ‘ya ‘yanmu sauya-sheka.” Inji sa

KU KARANTA: Okorocha ya yi magana kan yiwuwar Ibo su karbe mulki a zaben 2023

Majiyar ta ce PDP ba za ta yi sake wasu daga cikin ‘ya ‘yanta su tsere domin su yi takara a wata jam’iyyar ba. Wannan jigo na PDP ya ce tun kafin hukuncin kotun koli, sun san inda aka dosa.

Rahotannin sun ce masu neman mulki a PDP su na jira a kammala shari’ar 2019 ne kurum sannan su fara shiri. PDP dai ta rabu gida biyu; Wasu Gwamnoni da bangaren Nyesom Wike.

Yanzu haka ana ta rikici ne tun lokacin zaben majalisa tsakanin wadannan gwamnoni da Nyesom Wike wanda shi ne ya kakaba Uche Secondus a matsayin shugaban jam’iyya a baya.

Sauran gwamnonin na PDP da ke yakar Wike sun hada da wasu sababbin gwamnoni. Wike zai so a ba gwamnan Sokoto tuta ne a zaben 2023 inda su ke ganin za su samu saukin karawa da APC.

Sai dai jam'iyyar hamayyar ta fito ta yi jawabi ta bakin Kola Ologbondiyan, inda ta ce babu gaskiya a wannan rade-radin na 2023, kuma babu wani rikici da ya shiga tsakanin gwamnoninta.

Sakataren yada labaran jam'iyyar ya bayyana cewa babu abin da ke gaban PDP a yanzu illa ta lashe zabukan gwamnonin da za a yi a jihohin Bayelsa da Kogi a cikin wannan Watan mai-ci.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel