Okorocha: Akwai yiwuwar Inyamurai su karbi mulkin Najeriya a 2023

Okorocha: Akwai yiwuwar Inyamurai su karbi mulkin Najeriya a 2023

Tsohon gwamnan jihar Imo, Cif Rochas Okorocha, ya bayyana cewa babu wani abu wai shi mulkin Inyamurai a Najeriya. Tsohon gwamnan kasar Ibon ya bayyana wannan ne kwanan nan a Kano.

Yayin da tsohon gwamnan ya magana a jihar Kano a Ranar Asabar, 2 ga Watan Nuwamban 2019, ya yi watsi da abin da ake kira shugabancin Inyamurai, ya ce sai dai a ce shugabancin Najeriya.

Okorocha ya nuna cewa babu komai don an yi maganar shugaban kasa a 2023 ya fito daga yankin Ibo domin kuwa abu ne mai yiwuwa kamar yadda za a iya samun shugaban daga kowace Kabila.

“Ba na tunanin akwai wani abu mai suna mulkin Inyramurai a Najeriya, ba mu da wani abu mai suna mulkin Inyamurai, abin da mu ka sani shi ne mulkin Najeriya ko kuma shugaban Najeriya.”

KU KARANTA: An fara lissafin inda a mika mulki a PDP bayan 2019

“Abin da za su ka rika tambaya shi ne mai zai sa shugaban Najeriya ya fito daga yankin Ibo, idan wannan shi ne abin tambaya, to dama can maganar mutane ita ce damukaradiyya.” Inji Rochas.

Sanatan na Yankin Imo ta yamma ya kuma ce: “Mutanen Kudu maso Yamma ba zaman kansu su ke yi ba, su na cikin Najeriya, kuma za su iya samun mulki kamar yadda kowace kabila za ta iya”

“Babu matsala don wani ya tsaya takarar shugaban kasa a gwamnatin tarayya. A baya an rika bari son kai ya na tasiri a siyasar kasar wajen samun mulki, wanda bai haifar da da mai ido ba.”

Sanatan ya karkare kalaman sa da cewa dole kasar nan ta cigaba da rika tunanin lalubo duk wadanda za su iya yin mulkin da za su kai Najeriya ga matsayin da ya dace da ita a Afrika.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel