Almajiri: Gwamnonin Arewa su ka kawo cikas – Tsohon Shugaban UBEC

Almajiri: Gwamnonin Arewa su ka kawo cikas – Tsohon Shugaban UBEC

Tsohon Sakataren hukumar UBEC mai kula da matakin ilmi na kasa a Najeriya, Farfesa Ahmed Mohammed Modibbo, ya zargi gwamnonin Arewa da jawo tasgaro na kawo gyara a harkar ilmi.

Ahmed Mohammed Modibbo ya nuna cewa akwai laifin jihohi wajen cikas din da aka samu na shigar da tsarin Almajiranci cikin karatun zamani bayan kudin da gwamnatin baya ta kashe.

A yunkurin sa Almajirai cikin tsarin boko ne gwamnatin Goodluck Jonathan ta gina makarantu fiye da 100 a yankin Arewa saboda a gama tsarin karatun addini na gargajiya da na zamani.

Duk da irin biliyoyin da aka batar, wadannan makarantu sun kama hanyar lalacewa saboda rashin kula da watsi da su da aka yi bayan shekaru kamar yadda Farfesan ya bayyana wajen taro.

Babban Farfesan ya yi jawabi ne a wata takardarsa mai taken ‘Kafin a haramta karatun Almajiranci a Najeriya.” An gabatar da wannan lacca ne a sashen tarihi da bincike na ABU.

KU KARANTA: Yadda mu ka gano Ya ‘yanmu a Jihar Anambra – Iyayen Yaran Gombe

Tsohon shugaban na UBEC ya ce gwamnoni sun yi watsi da makarantun da gwamnatin tarayya ta ginawa Almajirai ne saboda sun so a ba su kudi a hannunsu domin su gina makarantun da kansu.

“Gwamnonin jihohi ba su ji dadin matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na yin wannan aiki ta hannun UBEC da gidauniyar ilmi na ETF ba domin sun so ne a ba su kudi, su bada kwangilar.”

Mohammed Modibbo ya ke cewa gwamnonin Arewa ba su rungumi wadannan makarantu da ke jihohinsu ba, har kuma a kai ga maganar cika alkawarin yarjejeniyar su da gwamnatin tarayya.

Malamin tarihin ya ce wancan lokaci ne na karshe da aka yi kokarin gyara Almajiranci da masu karatu ke fita nesa da gidajensu domin samun ilmi inda ya kawo salsalar tabarbarewar shirin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel