Wata mata ta shake 'ya'yan cikinta 2 har lahira bayan sun ki cin abincin da ta zuba wa guba

Wata mata ta shake 'ya'yan cikinta 2 har lahira bayan sun ki cin abincin da ta zuba wa guba

Dan uwan wata mata da ta kashe 'ya'yanta maza guda biyu ta hanyar shake su ya ce, tun asali an haifi 'yar uwar tasa da mugun hali.

Mutumin mai suna Martyn Barass ya ce 'yar uwarsa mai suna Sarah da abokin laifinta Brandon Machin ba kananan mugayen mutane bane, saboda tun suna yara burinsu shine su kashe abu mai rai.

Ya ce tun suna kanana suke son kashe dabbobin da ake ajiye wa gida don kawai suna jin dadin aikata kisa, lamarin da a karshe ya kai su ga kashe yaran; Tristan, mai shekaru 13, da Blake, mai shekaru 14.

Matar da abokin cin mushenta sun kashe yaran ne ta hanyar shake su, kwana daya kacal bayan sun tsallake cin abinci mai guba da mahaifiyarsu ta zuba.

Yanzu haka Sarah da Brandon na can gidan yari, inda aka tisa keyarsu tun watan Mayu bayan sun amsa lafin kashe yaran.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa nake kwanciya da maza 15 kowacce rana a Abuja - 'Yar shekaru 15

Martyn mai shekaru 34 ya bayyana cewa ya taba kiran jami'an sashen hulda da jama'a bayan ya hangi Sarah tana jan Blake a kasa kamar wani kayan wanki a shekarar 2010.

A cewar Martyn, Sarah da Machin sun shafe tsawon shekara 9 suna shirya yadda kashe 'ya'yan cikinta.

Sarah ta fara yunkurin kashe yaran ne ta hanyar saka musu guba a cikin abincinsu, amma sai suka kin cin abicin, lamarin daya sa mahifiyar tasu ta yanke shawarar kashe su ta hanyar shaka.

An Garza's da yaran zuwa asibiti domin a ceto rayuwarsu amma sai suka mutu bayan 12 kacal.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel