ICPC ta kama wasu jami'an N-SIP da laifin karkatar da makuden kudaden ciyar da dalibai a arewa

ICPC ta kama wasu jami'an N-SIP da laifin karkatar da makuden kudaden ciyar da dalibai a arewa

Hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta ta ICPC ta ce, ta cafke jami'an N-SIP biyu a jihar Kogi akan zarginsu da take da damfarar naira miliyan 68.

Wadanda ake zargin sune, Khadijat Karibo, wacce ita ce manajan shirin ciyarda 'yan makarantar da Adoga Ibrahim, wanda shima jigo ne a shirin ciyarda yaran makarantar a jihar.

A takardar da Rasheedat Okoduwa, mai magana da yawun hukumar ta bada, tace ICPC ta cafke jami'an biyu ne tare da hadin guiwar ofishin N-SIP kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Okoduwa tace, hukumar ta samu koken cewa, ana zargin jami'an biyu da waskar da kudaden da aka ware don ciyarda yara 'yan makaranta.

"Koke ne muka samu a kan cewa wani jigo da manajan shirin ciyarda yaran makaranta sun hada kai tare da waskar da makuden kudade da aka ware don biyan masu girki a jihar Kogi," in ji ICPC.

DUBA WANNAN: An karrama jaruma Fati Washa a Birtaniya

"Koken ya sanar cewa, mutane biyun sun debi kudin da aka ware don biyan masu girkin abincin yaran makaranta a jihar. Sun yi amfani da wasikun da suka saka hannu tare da bada umarnin a tura kudaden zuwa asusun bankuna goma mabanbanta don samar da wasu kayan girke-girken."

Mai magana da yawun hukumar yace, ba a samu wata kwakkwarar shaida tare da dalilin fitar da kudin ba.

"Koken ya kara da nuna cewa, rashin gaskiyar da suka yi har da hadin bakin wasu bankuna a jihar. A binciken da ICPC tayi, ya nuna cewa, koda siyan wasu kayan abinci za a yi, bukatar ta kan iso ne daga gwamnan jihar a inda zai bayyana abubuwan da ake bukata tare da yawansu ga shugaban shirin don amincewa," in ji takardar.

"Wannan takardar babu inda aka amince domin kuwa Ibrahim ya mika bukatar ne a watan Satumba amma babu wata shaidar amincewa." Takardar ta kara da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel