An damke Sojoji 3 da laifin garkuwa da mutane, da fashi

An damke Sojoji 3 da laifin garkuwa da mutane, da fashi

Hukumar yan sandan jihar Edo sun damke jami'an Sojojin Najeriya uku da wani mai farin hula daya da laifin garkuwa da mutane, da fashi da makami.

Tuni ana zargin wadannan Sojojin uku da aikata garkuwa da mutane a Agenebode, Fugar da wasu garuruwan jihar Edo.

Sojojin sune Kofura Collins Ameh 13NA/70/4960 na 3 Division, Jos; Lance Kofura Balogun Taiwo 13/NA/69/0369 na 35 Battalion, Katsina; da Evans Isibor 15/NA/73/1529 na Artillery Brigade, Owerri.

Mai farin hula cikinsu shine Goodluck Igbenebor.

An damke Kofura Ameh da Balogun ne bayan sun yi garkuwa da wani Mista Joseph Otono a watan Oktoba a garin Fugar, karamar hukumar Etsako ta tsakiya kuma sun kwace motarsa kirar Toyota Voltron.

Sojojin sun saki Mista Joseph bayan karban kudin fansa.

KU KARANTA: Kuma dai! An damke wata mata a tasha tana kokarin guduwa Onitsha da yaran Hausawan da ta sata

Dubunsu ya cika ne yayinda aka damkesu a Ehor, karamar hukumar Uhunmwode yayinda suke kokarin guduwa Legas domin sayar da motar.

An gano cewa su sukayi garkuwa da wata malamar makaranta a Fugar, Misis Catherine Izuagie, a watan Satumba, 2019.

Kakakin hukumar yan sandan jihar Edo, DSP Chidi Nwabuzor ya tabbatar wannan labari kuma ya ce an kaddamar da bincike cikin lamarin.

Nwabuzor yace: "Tabbas hukumar yan sandan jihar ta damke Sojoji uku da mai farin huka kan laifin garkuwa da mutane da fashi da makami. A yanzu haka shugaban SARS, SP Richard Balogun na bincikensu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel