Kuma dai! An damke wata mata a tasha tana kokarin guduwa Onitsha da yaran Hausawan da ta sata

Kuma dai! An damke wata mata a tasha tana kokarin guduwa Onitsha da yaran Hausawan da ta sata

Hukumar yan sanda a jihar Legas ta tabbatar da damke wata mata da ta sace yara maza biyu a watan jihar Arewa a tashar motar zuwa Onitsha, jihar Anambara, kudancin Najeriya.

A damke ta ne a tashar Chemist Bus Stop dake kusa da kasuwar Alaba a jihar Legas.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, DSP Bala Elkana, ya ce matar da mijinya a yanzu na hannun hukumar yan sanda.

Malam Abba Abdullahi wada idon shaida ne ya yi bayan kamar yadda Daily Trust ta ruwaito cewa wani dattijo ne ya ga matar tare da yara biyu a tasha suna kokarin shiga motar bas zuwa Onitsha.

Yace: "Dattijon ya ji yaran suna Hausa, sai ya kira Sarkin Hausawan yankin wanda ke kusa da unguwar Alaba Rago."

Da Sarkin Hasusawan ya samu labarin, sai ya aika jami'an tsaro da fadawansa wajen kuma aka damketa.

Bayan damketa, matar ta bayyana gaskiyar lamarin cewa wani mutum ne ya bata yaran a garin Jos.

DUBA WANNAN An damke Sojoji 3 da laifin garkuwa da mutane, da fashi

A yanzu an dauke matar da mijinta ofishin yan sanda na Ojo zuwa hedkwatan hukumar a Ikeja.

Ya kara da cewa mutane sun farga yanzu tun lokacin da aka samu labarin satar yara daga Arewa ana sayar da su a jihohin Inyamurai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel