A kafafen sadarwa mu ka gano inda yaranmu su ke – Iyayen Yaran da aka sace

A kafafen sadarwa mu ka gano inda yaranmu su ke – Iyayen Yaran da aka sace

Yara biyun da aka sace kwanaki a jihar Gombe aka tsere da su zuwa Anambra sun sadu da Iyayensu. Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton labarin yadda Yaran su ka hadu da Iyayen na su.

Iyayen wadannan yara sun bayyana cewa an sace yaran ne lokacin da su ke wasa da sauran yara a gidansu. Bayan 'yan makonni sai aka ji labarin bullarsu a wani Gari a cikin jihar Anambra.

Wadanda ‘yan sanda ke zargi da sace wadannan yara biyu su ne Patience Opia daga jihar Kuros Ribas, sai Ejece Obi daga Anambra da kuma Blessings John wata Mutumiyar jihar Bauchi.

“Wasu makwabtanmu su ka ga hotunan yaran a kafafen sadarwa na zamani ana cewa an ceto su a Anambra, sai su ka sanar da mu. Lokacin da mu ka tabbatar cewa su ne, sai mu ka zo Anambra.

KU KARANTA: Abin da ya sa na ke kwanciya da Maza 15 a duk rana ta Allah

“Mu ka shirya, mu ka tafi Anambra, mu ka yi kokari mu ka dawo da su. Lokacin da yaransu su ka hange mu, sai su ka ruga zuwa wajen mu.” Mahaifin wadannan yara ya fadawa Manema labarai.

Abdulaziz Suleman, wanda shi ne Mahaifin wadannan ‘ya ‘ya ya yi murnar yadda Ubangiji ya sake sada su da Yaran bayan kwanaki ashirin da sace su inda har an fara shirin saida su ga wasu.

Opia ta bayyanawa Daily Trust cewa Blessings John ce ta kawo mata wadannan yara da nufin a sa su a makaranta. John ta fadawa Opia cewa wadannan ‘ya ‘yanta ne da kuma wata ‘Yaruwarta.

Rahotanni sun ce mutanen da su ka sace wadannan kananan yara daga Gombe sun fara yunkurin saida su a kan kudi N750, 000 kafin asirinsu ya tonu a sanadiyyar kafafen yada bayanan zamani.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel