Enugu: Alkalin kotun daukaka kara ya tsige Hon. Ogbee, ya ba APC nasara

Enugu: Alkalin kotun daukaka kara ya tsige Hon. Ogbee, ya ba APC nasara

- Kotu ta nemi INEC ta karbe satifiket din nasarar Lazarus Ogbee

- Alkali ya tabbatar da cewa Chinedu Ogah ne ya lashe zaben 2019

- An tabbatar da hukuncin da kotun sauraron korafin zabe ya yi

Mun ji labari cewa kotun daukaka kara da ke Garin Enugu, a jihar Enugu, ya tsige Honarabul Lazarus Ogbee daga kan kujerar majalisar wakilan tarayya na Mazabar Ikwo da Ezza ta Kudu.

Kotun daukaka kara ya yi hukuncin cewa a karbe shaidar nasarar da aka ba ‘dan takarar PDP, a mikawa Chinedu Ogah wanda ya tsayawa jam’iyyar APC mai adawa a jihar Enugu takara a 2019.

Alkali mai shari’a Ignatius Agube, shi ne ya jagoranci wannan shari’a a zaman da su ka yi a Garin Enugu. Agube ya tabbatar da hukuncin da kotun sauraron karar zaben 2019 ya yi kwanakin baya.

KU KARANTA: Takarar Shugaban kasa a zaben 2023 ta fara raba kan ‘Ya ‘yan PDP

Babban kotun ya jaddada cewa Chinedu Ogah shi ne ainihin wanda ya lashe zaben kujerar Mazabun Ikwo da Ezza a majalisar tarayya a zaben da 23 ga Watan Fubrairun shekarar bana.

Bayan haka kuma Alkalin babban kotun ya tabbatar da nasarar Honarabul Sylvester Ogbaga mai wakiltar Izzi da Abakaliki a majalisar tarayyar. Kotu ta yi fatali da korafin da APC ta kawo mata.

Sylvester Ogbaga ya sake doke ‘dan takarar APC, Maurice Uchenna Nshii, wanda yake kalubalantar nasarasa a kotu. Ogbaga ya zama wanda ya fara zuwa majalisa sau hudu a Ebonyi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel