NAF ta tarwatsa mayakan ISWAP tare da maboyarsu

NAF ta tarwatsa mayakan ISWAP tare da maboyarsu

Rundunar sojin saman Najeriya tace, jiragen yakinta sun tarwatsa maboyar mayakan ISWAP a Arrinna Ciki da ke gaban tafkin Chadi a arewacin jihar Barno, kamar yadda gidan talabijin din Channels ya ruwaito.

Daraktan hulda da jama'a da yada labarai na rundunar sojin, Air Commodore Ibikunle Daramola, ya bayyana hakan ne a wata takarda da ya mika ga gidan talabijin din Channels a ranar Lahadi.

Yayi bayanin cewa, rundunar sojin ta musamman ta Air Task Force ta Operation Lafiya Dole ta kai samamen ne ta jiragen yakinta a ranakun Juma'a da Asabar inda ta hallaka mayakan ISWAP din.

Kamar yadda Daramola ya sanar, hakan ya biyo bayan bayanan sirri ne da rundunar ta samu na cewa mayakan na amfani da wajen ne don buya tare da shirin kai hari ga jami'an tsaron.

DUBA WANNAN: Wata sabuwa: Kungiyar 'yan kasuwan Ghana ta rufe shagunan kasuwancin 'yan Najeriya

Ya bayyana cewa, samamen na ranar Juma'an ya biyo bayan rahotannin sirri da suka samu tare da ganin wasu ababen hawan mayakan da suka yi a kasan bishiyoyin yayin da suka yi leken asiri ta jiragen yaki.

Mai magana da yawun rundunar sojin saman yace, "Runduna ta musamman din ta dau jiragensu ne inda suka kai harin da suka samu nasarar halaka 'yan ta'addan da kuma ababen hawansu."

"Hakazalika, sojin sun kara kai samame a ranar 1 ga watan Nuwamba bayan da aka lura da lamurransu sun dawo wasu yankunan maboyarsu. Hakan kuwa ya jawo aka kara tura jiragen yakin maboyar inda suka tarwatsa 'yan ta'addan tare da gidajensu," ya kara da cewa.

Rundunar sojin saman, kamar yadda shugaban ya sanar, zasu tsaya tsayin daka wajen ganin sun kawo karshen duk wani ta'addanci da ya addabi yankin arewa maso gabas din tare da halaka ragowar maboyarsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel