Kasafin kudi: Sanatoci sun bukaci ganin Minista da Shugaban NEPZA

Kasafin kudi: Sanatoci sun bukaci ganin Minista da Shugaban NEPZA

Kwamitin kasuwanci da hada-hada a majalisar dattawa ta bukaci ganin Ministan kasuwanci, Niyi Adebayo, da kuma shugaban hukumar da ke kula da fitar da kaya waje, Terhembe Nongo.

Kamar yadda mu ka ji, Sanatoci sun bukacin ganin Mai girma Ministan tare da Mukaddashin Darektan hukumar NEPZA ne kan kudin da suka warewa wani kamfani mai zaman kansa.

Ma’aikatar kasuwanci ta yi kasafin Naira biliyan 15 ga wani kamfani mai zaman kansa a cikin kasafin kudinta. Sai dai kuma Ma’aikatar ta gaza bada gamsashen bayani kan wannan kudi.

Shugabar wannan kwamiti a majalisar, Rose Oko, ta ce sun aika wannan sammaci ne bayan ganin Ministan da babban Sakataren ma’aikatar sun ki bada bayanin da ake bukata game da kamfanin.

KU KARANTA: Buhari zai iya neman ya zarce a kan mulki bayan 2023 - Galadima

A lokacin da aka yi kokarin kare kasafin kudin ma’aikatar a gaban majalisa, Adebayo da sauran manyan jami'ai ba su iya bayyana wadanda su ka mallaki wannan kamfani mai zaman kansa ba.

Sanata Oko ta sanar da kwamitin kasafi cewa da ta nemi NEPZA ta yi mata bayani game da yadda ta ware kudi ga wannan kamfani, sai hukumar tace an yi hakan ne tun kafin a bude kamfanin.

“An yi wa wannan kamfani rajista ne a 2018, amma an riga an ware kudin tun 2017, an zuba kudin cikin CBN. A karshe ma an saki biliyan 15 daga wannan kudi zuwa kamfani kwanan nan.”

Yanzu haka dai ana ta faman aiki a kan kasafin shekara mai zuwa. Majalisar tarayya ta ci burin ganin an kammala wannan aiki kafin lokacin tafiya hutun bikin kirismeti a karshen Disamba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel