‘Yan Sanda sun kama Shugaban kwamitin tsaron PDP da makamai

‘Yan Sanda sun kama Shugaban kwamitin tsaron PDP da makamai

Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust dazu nan cewa ‘yan Sanda sun tabbatar da cewa sun kama shugaban kwamitin harkar tsaro na yakin neman zaben gwamnan PDP a jihar Kogi.

Jami’an tsaro sun damke Suleiman Ejeh Abutu mai ritaya ne tare da wasu mutum shida da zargin rike bindigogi da harsashi ba da izni ba. An damke su ne a cikin karamar hukumar Dekina.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kogi, Hakeem Busari ya ce wasu Dakarun ‘yan sanda daga Hedikwata ne su ka kai samamen da su ka cafke ACP Suleiman Ejeh Abutu da sauran jama’ansa.

Bayan wannan Tawaga ta musamman ta cafke Jagoran na yakin neman zaben PDP, ta wuce da su zuwa babban birnin tarayya Abuja. Watakila a can ne za a gabatar da su kan zargin da ke kansu.

KU KARANTA: Hadimin Gwamna ya rasa kujerarsa bayan ya yada bayani ba daidai ba

Jam’iyyar PDP ta fito ta yi magana bayan aukuwar wannan lamari. Mataimakin Darektan yada labarai na jirgin yakin neman PDP a zaben Kogi, Austin Okai, ya maida martani a Ranar Asabar.

Mista Austin Okai ya bayyana cewa akwai ‘burbushin siyasa’ a lamarin. Okai ya zargi jam’iyyar APC mai mulki da amfani da jami’an ‘yan sanda domin su yi kokarin ganin bayansu a zaben.

Darektan na PDP ya ce APC ta hada-kai ne da jami’an tsaro saboda a hana su yawo yayin da ake shiryawa zaben gwamna a cikin Watan nan na Nuwamba inda manyan jam’iyyun za su kara.

Jam’iyyar PDP mai hamayya ta ce yanzu haka akwai yunkurin da Jami’ai ke yi na damke manyan ‘ya ‘yan ta irin su Sanata Yahaya Ugbane da kuma Alex Kadiri da sauransu kafin Ranar zaben.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel