Kaiwa gwamnan Edo haro: Mataimakin gwamna ya kare kansa, ya ce Oshiomhole ne ya gayyaci matasan

Kaiwa gwamnan Edo haro: Mataimakin gwamna ya kare kansa, ya ce Oshiomhole ne ya gayyaci matasan

Babban sakataren yada labarai na mataimakin gwamnan Edo, Musa Ebomhiana ya musanta zargin da ake yi wa mai gidansa, Kwamared Philip Shaibu da hannu cikin harin da aka kaiwa Sarkin Legas da wasu manyan baki a gidan shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole.

Ya ce mataimakin gwamnan yana tare da tawagar gwamnan lokacin da abin takaicin ya faru saboda haka ba bu yadda za a ce shine ya jagoranci wadanda suka kai harin kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Ya ce, "Babu yadda za a ce mataimakin gwamna ne ya janyo wannan aika-aikan. Gwamnan, mataimakinsa da Sarkin Legas da tawagarsu suna kofar gidan shugaban jam'iyyar mu, Adams Oshiomhole don kai masa ziyarar ban girma tunda sun zo jiharsa.

DUBA WANNAN: Babbar magana: Shugabannin APC sun nemi Buhari ya tsige wani ministansa

"Abin mamaki, wasu mutane masu tarin yawa da suka taru a kofar gidan sun kaiwa tawagr hari inda suka lalata motocci uku. Hakan yasa dole tawagar suka juya cikin gaggawa suka koma cikin harabar jami'ar jihar.

"Saboda haka, ta ya ya za a ce mataimakin gwamna ne na dauki nauyin wadanda za su kai masa hari? Hasali ma, Kwamared Adams Oshiomhole da kansa ne ya gayyace su."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel