Rufe iyakoki ya taimaka wajen rage shigo da makamai Najeriya - Shugaban DSS

Rufe iyakoki ya taimaka wajen rage shigo da makamai Najeriya - Shugaban DSS

Shugaba Hukumar DSS, Magaji Bichi, ya ce rufe iyakokin da Najeriya da gwamnatin tarayya tayi ya taimaka wajen rage fataucin makamai kuma ya taimakawa jami'an tsaro wajen lura da shiga da ficen mutanen da ka iya zama kalubale ga zaman lafiyar kasa.

Mista Bichi ya bayyana hakan ne a taron yaye daliban ilimin leken asiri da Abuja.

Ya roki gwamnati ta sanyawa iyakokin katangar karfe har sai lokacin da abubuwa suka daidaita.

Yace: "Kulle iyakokinmu ya fara haifar da 'da mai ido duk da soke-soken da akeyi. Rufe iyakokin kawo yanzu ya taimaka wajen hana fasa kwabrin kayyayaki da makami zuwa kasar. Hakazalika ya taimaka wajen lura da shiga da ficen mutanen da ka iya kawo matsalar tsaro kasar nan."

Shugaban DSS ya yi kira ga daliban da ake yayewa su yi amfani da ilimin da suka samu a wuraren aikinsu domin taimakawa gwamnati wajen dakile matsalolin tsaro.

DUBA WANNAN Harin da aka kaiwa gwamnan Edo: Laifin mataimakin gwamna Philip Shaibu ne - Oshiomole

Za ku tuna cewa a ranar 21 ga Agusta, gwamnatin tarayya ta rufe iyakokin Najeriya hudu domin kawo karshen fasa kwabri domin inganta tattalin arzikin kasa.

A cewar mai baiwa shugaban kasa shawara kan tsaro, Babagana Monguno, ba za'a bude iyakokin ba har sai an cimma manufa.

Hakazalika gwamnan bankin CBN, Godwin Emefiele, ya kwadaitar da gwamnati ta bar iyakokin a rufe har tsawon shekaru biyu masu zuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel