Harin da aka kaiwa gwamnan Edo: Laifin mataimakin gwamna Philip Shaibu ne - Oshiomole

Harin da aka kaiwa gwamnan Edo: Laifin mataimakin gwamna Philip Shaibu ne - Oshiomole

Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress, Kwamred Adams Oshiomhole, ya nemi gafarar sarkin Legas, Oba Rilwan Akiolu; gwamnan Legas, Godwin Obaseki; da Cansalan jami'ar Edo, Dr. Makanjuola, ka harin da aka kai musu a gidansa.

Oshiomole ya ce matasan da suka kaiwa gwamna da sarkin Legas wannan hari wasu yan barandan ne da suka dira jami'ar bisa umurnin mataimakin gwamnan jihar, Philip Shaibu.

Oshiomole ya ce an fara samun tashin hankali a unguwar ne ranar Juma'a bayan mataimakin gwamnan ya shigo da yan baranda domin cin mutuncin abokan hamayya.

A jawabin da kakakinsa, Mista Simon Ebegbulem, ya saki, Oshiomole ya ce ko a ranar Alhamis da ya halarci taron lakca a jami'ar, ta bayan fagge ya fita saboda gudun cin mutuncin da matasan ke shirin yi.

Oshiomole ya ce lokacin da bakin da aka gayyata suka iso dakin taro misalin karfe 11:30 na safe, mataimakin gwamnan ya dira jami'ar da yan babur da yan daba 200.

DUBA WANNAN Jami'an Soji sun cika hannu da masu garkuwa da mutane 6 a Abuja

A cewarsa: "Jami'an tsaro sun hanasu shiga amma sai suka fara yiwa jami'an tsaron barazana. Daga karshe sun bar mataimakin gwamnan shi kadai ya shiga."

Bayan lakcan, Oshiomole ya gayyaci Sarkin Legas da Cansalan gidansa wata liyafa gidansa da ke kusa da jami'ar.

"Yayinda suka fara shigowa cikin gidan, sai matasan Iyamho suka mamaye kofar shiga domin hana cin mutuncin Oshiomole."

"Amma da suka hango wasu matasa biyu Andrew Momodu da Osaigbovo Iyoha cikin motar da gwamnan ke ciki, sai sukayi kokarin hana motar shiga saboda matasan ne suka kaiwa Oshiomole hari a makon da ya gabata."

"Ana cikin wannan dambarwan ne yan barandan da mataimakin gwamnan ya kwaso suka fara fasa motoci."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel