Jami'an Soji sun cika hannu da masu garkuwa da mutane 6 a Abuja

Jami'an Soji sun cika hannu da masu garkuwa da mutane 6 a Abuja

Dakarun Sojin Najeriya sun damke shugaban wata kungiyar yan bindiga, Shehu Jatau, tare da yaransa biyar a wani Otal a kwaryar birnin tarayya Abuja.

Jatau da yan kungiyarsa ne suka addabi birnin tarayya da fashi da kuma garkuwa da mutane.

A ranar Asabar, hukumar Sojin ta bayyana cewa binciken da aka fara kaddamarwa ya nuna cewa sun kasance masu tayar da zaune tsaye a jihar Flato amma suka koma Abuja domin garkuwa da mutane da fashi.

Jami'in yada labarai na hukumar Soji, Kanal Aminu Iliyasu, a jawabin da ya saki ya tabbatar da damkesu.

Iliyasu yace: "Wani kasurgumin shugaban yan bindigan kabilar Tarok, Shehu Jatau, tare da abokan aikinsa biyar sun shiga hannu a sintirin da aka kai musu cikin dakin Otal cikin garin Abuja."

Bincike ya nuna cewa yan barandan sun kasance masu tayar da tarzoma a jihar Plateau da aka yi asarar rayuka da dukiyoyin biliyoyin Naira."

"Amma da aka samu zaman lafiya a jihar, sai suka koma garkuwa da mutane, sace-sace da kaiwa mutane hari."

A bangare guda, dakarun 2 Battalion yayinda sintiri tsakanin kauyen Falwaya da Gayam a karamar hukumar birnin gwari na jihar Kaduna sun ceto mutane bakwai da aka sace."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel