Okorocha ya bayyana abinda zai faru da APC bayan 2023

Okorocha ya bayyana abinda zai faru da APC bayan 2023

- Sanata Rochas Okorocha ya ce rikicin cikin gida na shugabanci a jam'iyyar APC zai jawa jam'iyyar cikas a zaben 2023

- Okorocha ya bayar da misali da rikicin da ke tsakanin shugaban jam'iyyar na kasa Adams Oshiomhole da Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo

- Dan majalisar ya shawarci Oshiomhole da Obaseki su sasanta kansu domin duk jam'iyyar da ba ta hada kanta ba ba za ta yi nasara ba

Sanata Rochas Okorocha ya gargadin cewa akwai yiwuwar jam'iyyar APC za ta rasa mulki a zaben 2023 muddin ba a sasanta rikicin cikin gida da ke afkuwa tsakanin wasu shugabanin jam'iyyar.

The Nation ta ruwaito cewa Okorocha ya yi wannan gargadin ne a ranar Asabar 2 ga watan Nuwamba a jihar Kano inda ya bayar da misali da rikicin da shugaban jam'iyyar na kasa, Adams Oshiomhole ke yi da gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki.

DUBA WANNAN: Shekau ya sake fitar da sabon sakon murya, ya gargadi wani lauya a Borno

Sanatan ya ce kamata ya yi a rika samun hadin kai tsakanin 'yan jam'iyya inda ya ce yawaitar rikicin cikin gidan na nuna cewa 'ya'yan jam'iyyar ba su da akida iri guda.

Ya shawarci Oshiomhole da Obaseki su sasanta junansa inda ya ce duk jam'iyyar da babu hadin kai a cikin ta ba za ta yi tasiri ba.

Ya ce a halin yanzu jam'iyyar ta APC ba ta da wani gwani da za ta amfana da farin jininsa a 2023 kamar yadda farin jinin Shugaba Muhammadu Buhari ya bawa jam'iyyar nasara a 2015.

Ya ce ya zama dole jam'iyyar ta samu jagoranci nagari idan har tana son ta cigaba da rike mulkin kasar bayan wa'adin Shugaba Buhari ya kare a 2023.

A wani rahoton, Legit.ng ta kawo muku cewa tsohon shuganan kungiyar 'yan kabilar Ijaw, Farfesa Kimse Okoko ya ce idan ana son hadin kai bai kamata wata kabila a kasar ta yi hamayya da 'yan kabilar Ibo ba a 2023.

Farfesan ya yi wannan jawabin ne yayin da ya ke zantawa da jaridar daily Sun. Okoko ya ce kiraye-kirayen da wasu 'yan Arewa ke yi na cigaba da mulkar kasar na iya tayar da zaune tsaye.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel