Shikenan ta faru ta kare: Wata daya da mutuwar mahaifiyar Nnamdi Kanu mahaifinsa shima ya ce ga garinku nan

Shikenan ta faru ta kare: Wata daya da mutuwar mahaifiyar Nnamdi Kanu mahaifinsa shima ya ce ga garinku nan

- Ba a kai ga binne mahaifiyarsa ba sai kwatsam aka sanar da shi cewa mahaifinsa shima ya mutu

- Wannan abu dai ya faru ne da shugaban masu gwagwarmayar kafa yankin Biafra wato Nnamdi Kanu

- A watan Satumbar nan ne dai da ya gabata Nnamdi Kanu ya sanar da cewa mahaifiyarsa ta mutu, sannan ya dora alhakin mutuwar ta kan gwamnatin tarayya

A yayin da Nnamdi Kanu yake shirye-shiryen jana'izar mahaifiyarsa a binne ta, kwatsam sai jin wani mummunan labari yayi na cewa mahaifinsa da ya rage shima ya mutu.

Mahaifin shugaban 'yan gwagwarmayar kafa kasar Biafra, Mr. Kany ya mutu ranar Alhamis dinnan 31 ga watan Oktobar shekarar 2019, a babban asibitin tarayya na garin Umuahia babban birnin jihar Abia, inda aka kai shi yake jinya na tsawon makonni biyu.

Idan ba a manta ba makonnin da suka gabata Nnamdi Kanu ya sanar da mutuwar mahaifiyarsa Ugoeze Sally Meme Kanu wacce ta sha fama da rashin lafiya a wani asibiti dake kasar Jamus, mahaifiyar ta sa ta mutu a watan Satumban da ya gabata.

KU KARANTA: Ni da kudi na nake yin harkar fim ba 'yar ku ci ku bani bace - Jaruma Safna Aliyu ta yi martani mai zafi

Wannan shine lokaci da Nnamdi Kanu ba zai taba mantawa da shi ba a rayuwar shi, wanda a baya ya zargi gwamnatin tarayya da hannu a mutuwar mahaifiyarsa, saboda abubuwan da hukumomin tsaro suka yi a garinsu watannin da suka gabata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel