Baturen Amurka ya kashe budurwa 'yar Najeriya bayan ya nemi ta aureshi taki amincewa

Baturen Amurka ya kashe budurwa 'yar Najeriya bayan ya nemi ta aureshi taki amincewa

- Wani mutumi dan kasar Amurka ya kashe wata budurwa 'yar Najeriya

- Mutumin ya kashe budurwar ne saboda taki amincewa da maganar aure da yayi mata

- An bayyana cewa budurwar da saurayin sun hadu a wani shafin soyayya ne na yanar gizo mai suna Plenty Fish

Wani mutumi dan kasar Amurka ya kashe wata budurwa 'yar Najeriya wacce suka hadu a shafin soyayya na yanar gizo-gizo bayan ya nemi ta aure shi taki amincewa.

Mutumin dan shekara 38 dake garin Georgia, dake kasar Amurka an bayyana sunan shi da Antonio Wilson, an kama shi da laifin kashe budurwar 'yar Najeriya mai suna Fabiola Thomas mai shekaru 39 wacce taki amincewa da bukatar auren shi.

Abokiyar zaman Fabiola ta samu gawarta a cikin bandaki a gidansu dake Atlanta Newtown, cikin gaggawa ta sanar da hukumar 'yan sanda, an dauke ta zuwa asibiti inda aka bayyana cewar ta mutu.

KU KARANTA: Ni da kudi na nake yin harkar fim ba 'yar ku ci ku bani bace - Jaruma Safna Aliyu ta yi martani mai zafi

A yadda aka ruwaito, Fabiola da Wilson sun hadu a shafin soyayya na yanar gizo mai suna Plenty Fish, mai magana da yawun hukumar 'yan sandan Sean Thompson ya ce mutuwar budurwar yana da nasaba da kin amincewa da auren shi.

An bankado cewa Wilson ya shirya baiwa Fabiola zobe sai ta bayyana mishi cewa ba ta so kuma kada ya sake ya zo gidansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel