Yanzu-Yanzu: An kaiwa wani gwamna da sarki hari a gidan Oshiomhole

Yanzu-Yanzu: An kaiwa wani gwamna da sarki hari a gidan Oshiomhole

- Alhini da al'ajabi ya shiga zukatan mutane a jihar Edo a ranar yau Asabar

- Hakan kuwa ya faru ne sakamakon hari da wasu da ake zargin bata-gari ne suka kaiwa gwamna, basarake da kuma wani mai hannu da shuni a gidan shugaban APC ta kasa

- Kamar yadda majiya daga jami'an 'yan sanda ta sanar, an gayyacesu cin abincin rana ne a gidan shugaban APC

Wasu bata- gari sun kaiwa tawagar Gwamna Godwin Obaseki, sarkin jihar Legas, Rilwan Akiolu da shugaban Caverton Offshore Support Group, Aderemi Makanjuola hari.

An kai musu harin ne yayin da suka shiga gidan shugaban jam'iyyar APC ta kasa, Adams Oshiomhole, jim kadan bayan bikin yayen dalibai na farko na jami'ar Edo da ke Iyamho, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Abdulmumin Kofa ya yi martani kan hukuncin kotun daukaka kara na soke zabensa

An nada Makanjuola a matsayin shugaban jami'ar a bikin yayen daliban.

Majiya daga jami'an 'yan sanda ta ce, Oshiomhole ya gayyacesu cin abincin rana ne yayin da wadanda ake zargin bata-garin suka kai musu hari.

Kamar yadda ganau ba jiyau ba suka sanar, rigimar ta kaure ne da taimakon mataimakin gwamnan jihar, Philip Shaibu, wanda ake zargin cewa ya yi wa 'yan achaba akalla dari biyu jagora zuwa wajen yayen daliban a safiyar yau Asabar.

Taimakon jami'an tsaron gwamnan ne ya hana yin kare-jini, biri-jini a wajen saboda ababen hawa da yawa a wajen an lalatasu.

An kori mataimakin gwamnan da 'yan achaban sakamakon barkonon tsohuwa da jami'an 'yan sanda suka watsa musu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel