Yanzu-yanzu: Buhari ya kammala Umrah, ya shilla Landan hutawa

Yanzu-yanzu: Buhari ya kammala Umrah, ya shilla Landan hutawa

Jirgin shugaban kasan Najeriya Airforce 001 ta tashi daga babban filin jirgin Sarki Abdul’aziz dake Jeddah zuwa birnin Landan, kasar Ingila domin hutu.

Legit.ng ta smau labari daga bakin hadimin Buhari kan sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmad, inda yace:

"Bayan nasarar kammala halartan taron Future Investment Initiative (#FII2019) a Riyadh da Umrah a Makkah, shugaba Buhari ya tashi daga Jiddah zuwa Landan."

Da yammacin Alhamis, Shugaba Muhammadu Buhari ya isa birnin Makkah, domin gabatar da ibadar Umrah bayan kammala halartan taron sanya hannu jari na tsawon kwana uku a birnin Riyadh.

Shugaba Buhari ya dira filin jirgin saman Sarki AbdulAziz ne misalin karfe 7:05 na Magariba.

A ranar Litinin ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bar Abuja zuwa birnin Riyadh na kasar Saudiyya domin halartar wani taro na masu saka hannu jari (FII) da hukumar samar da kudaden kasuwanci ta kasar Saudiyyya (PIF) ta shirya.

A cikin tawagar akwai karamin ministan harkokin kasashen waje, Zubairu Dada, ministan kamfanoni, kasuwanci da saka hannu jari, Niyi Adebayo, karamin ministan man fetur, Timipre Sylva, da ministan harkokin sadarwa, Dakta Ibrahim Pantami.

Mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya), darekta janar na hukumar NIA, Ambasada Ahmed Rufa'i Abubakar Kyari, da shugaban kamfanin dillancin man fetur na kasa (NNPC), Mele Kolo Kyari, na cikin tawagar shugaba Buhari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel