Buhari na iya neman zarcewa kan mulki karo na uku - Buba Galadima

Buhari na iya neman zarcewa kan mulki karo na uku - Buba Galadima

Wani tsohon shakikin shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma tsohon shugaban jam'iyyar APC, Alhaji Buba Galadima, ya yi kira ga 'yan Najeriya da kada su yi mamaki idan Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi kujerar shugabncin kasa a shekarar 2023.

Galadima, wanda a halin yanzu abokine ga Alhaji Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma dan takarar kujerar shugabancin kasa karkshin jam'iyyar PDP a zaben 2019, ya ce akwai masu angiza shugaban kasar don ya kara neman zarcewa kujerarsa.

A tattaunawar da yayi da jaridar The Sun, galadima ya yi ikirarin cewa, Buhari ya killace ma'aikatar shari'a, a don haka ne ya yi wucewarsa zuwa Saudi Arabia ana gobe kotun koli za ta duba shari'arsa da Atiku.

Kamar yadda ya sanar, "Ban taba ganin mummunan lamari ba kamar abinda muke fuskanta a Najeriya a yau karkashin jagorancin gwamnatin APC da shugabancin kasar Muhammadu Buhari. Har kuwa lokacin mulkin soji, 'yan Najeriya basu taba gurzuwa kamar haka ba".

DUBA WANNAN: Jigo a jam'iyyar APC ya yi mummunan hadarin mota, ya sha da kyar

"A halin yanzu shuagaban kasa ya garzaya Saudi Arabia kuma zai zarce Landan. Hakan na nuna halin shugaba nagari kuwa? Buhari na tafiye-tafiye amma ya bar 'yan Najeriya a cikin matsanancin talauci," in ji Galadima.

"Buhari ya mallake ma'aikatar shari'a kuma yana tsammanin babu abinda zai faru. Yana kuma da tabbacin zai yi nasara a kotun. Gwamnatinsa ta gurbata ma'aikatar shari'a. hakan kuwa Hakan kuwa barazana ce ga damokaradiyyarmu da kujma kasarmu," Buba ya kara.

"Yan siyasa da yawa zasu kunyata. Ubangiji kadai yasan abinda zai faru a 2023. Tsaf zai iya shiga ayarin amsu neman kujerar shugabncin kasar nan a shakerar 2023. Amma kuma abinda 'yan siyasar nan basu sani ba shine, suna fallasa kansu ne tare da nuna gazawarsu wacce zata iya zam nasara da makiyansu ko abokan hamayyarsu na siyasa", in ji Galadima.

Amma kuma, kundin tsarin mulki bai aminta da kara zaben shugaban da yayi mulki har sau biyu ba a wani mataki na zababbu. Amma kuma anyi yunkurin gyara kundin tsarin mulkin yayin mulkin Obasanjo wanda hakan yaci tura.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel