Kuda wajen kwadayi: Ficik wata budurwa ta cirewa wani mutumi mazakuta da hakori a yayin da yake kokarin yi mata fyade

Kuda wajen kwadayi: Ficik wata budurwa ta cirewa wani mutumi mazakuta da hakori a yayin da yake kokarin yi mata fyade

- Wata mata da wani mutumi yayi garkuwa da ita ta samu ta sha da kyar bayan yayi kokarin yi mata fyade

- Matar dai ta samu ta cire masa mazakuta ne da hakori sannan ta caka masa wuka a duwawu a yayin da ya tilasta sai ya kwanta da ita

- An ruwaito cewa mutumin yayi garkuwa da ita ne daga cewa zai rage mata hanya daga wani gidan mai da yaje shan mai a garin Greenville

Wata mata da aka yi garkuwa da ita an ruwaito cewa ta cirewa wanda ya sato ta mazakuta a yayin da yayi kokarin yi mata fyade.

Matar ta yi fada da wannan mutumi mai suna Dennis Slaton mai shekaru 61, inda ta daga baya kuma ta daba masa wuka ta fito titi tsirara duk jikinta faca-faca da jini, a rahoton da 'yan sandan South Carolina suka bayar.

Slaton wanda dama can ya sha aikata laifuka makamantan haka ana tuhumarsa da laifin garkuwa da ita da kuma kokarin yi mata fyade.

Yayi garkuwa da matar ne a cikin garin Greenville a lokacin da ya tsaya a gidan mai zai sha mai sai ya nemi ya rage mata hanya a ranar 8 ga watan Agustan da ya gabata.

KU KARANTA: Ina ji ina gani haka 'yan sanda suka dinga bi da bi a kaina suna zina dani saboda bani da cin hancin da zan ba su - In ji wata budurwa

Maimakon ya ajiye ta a inda ta nuna masa tana son sauka sai ya fara yi mata barazana da wuka ya dauketa zuwa gidan shi, kamar dai yadda shugaban hukumar 'yan sanda na Greenville ya bayyana.

Bayan ya tilasta matar ta bishi gida, sai yayi kokarin yin lalata da ita tare da yi mata barazanar kisa, kamar dai yadda rahoton ya ruwaito.

Amma sai matar tayi sa'a ta cije shi a mazakuta, sannan tayi amfani da wukar tashi ta daba masa a duwawu daga nan ta gudu daga cikin gidan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel