Babbar magana: Shugabannin APC sun nemi Buhari ya tsige wani ministansa

Babbar magana: Shugabannin APC sun nemi Buhari ya tsige wani ministansa

Shugabannin jam'iyyar APC na jiha sun yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sauke ministan Niger Delta, Godswill Akpabio, a kan zargin wasu lamurransa da ake yi kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Kamar yadda shugabansu Ali Dolari da sakatarensa, Ben Nwoye suka sanar bayan kammala taro a Asaba, shugabannin sun saka ayar tambaya a kan yadda ministan ke shiga wasu al'amuran hukumar habaka lamurran yankin Niger Delta.

Sun ce, "Mun sa ayar tambaya akan yadda Akpabio ya hanzarta nada kwamitin rikon kwarya wanda yayi karen tsaye ga dokokin NDDC. Kamar yadda ya nada wani Dr Cairo Ojougboh a matsayin mukaddashin daraktan aiyuka. Amma kuma dokokin kafa NDDC din ta ce, cike wannan gurbin sai injiniya,"

DUBA WANNAN: Kujerar Sanata: PDP ta sake lallasa tsohon gwamnan APC a kotun daukaka kara

Me Akpabio ke nufi da ya hanzarta zaben Dr Joy Nunieh wanda shine ke wakiltar jihar Rivers a matsayin mukaddashin daraktan kwamitin rikon kwaryarsa?

Amma kuma, Akpabio ya jajanta cewa, yankin Niger Delta bashi da cigaba ta bangaren kayan more rayuwa duk kuwa da yawan kudaden da ake narkarwa don yankin.

Sun ce, 'yan kwangila 71 sun koma bakin aiki bayan binciken da Majalisar Dattawa ta yi akan lamurran habaka yankin Niger Delta.

Shugabar bangaren yada labarai ta ma'aikatar, Patricia Dewortshe, ta sanar sa hakan ne a ranar Laraba. Ta ce ministan ya yi wannan bayanin ne a yayin da ya karbi bakuncin kwamitin magoya bayan shugaban kasa na yankin kudu wadanda suka samu jagorancin tsohuwar 'yar majalisar wakilai, Doris Oboh, a Abuja.

Ta ce, Akpabio yayi kira ga kwamitin magoya bayan shugaban kasan da su ginu akan soyayyar juna ta yadda zasu hada kai wajen habaka yankin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel