'Yan sanda sun cafke mutum 6 da ake zargi da harbe wani jigon PDP

'Yan sanda sun cafke mutum 6 da ake zargi da harbe wani jigon PDP

Sashi na musamman na binciken laifukan kisan kai na hukumar 'yan sandan jihar Rivers, sun tabbatar da kammala bincike a kan mutane shida da aka zarginsu da kisan wani shugaban jam'iyyar PDP a Alakahia, karamar hukumar Obio-Akpor ta jihar Rivers.

Kamar yadda hukumar ta sanar, za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.

An kamasu ne da hannu a kisan wani shugaba, Anele Nworzuruka, wanda aka harbe a gaban matarsa da 'ya'yansa uku a ranar 21 ga watan Satumba, 2019.

Mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar Rivers, Nnamdi Omoni, ya ce an cafke mutane shidan da ke da hannu a cikin kisan.

'Yan sanda sun cafke mutum 6 da ake zargi da harbe wani jigon PDP

'Yan sanda sun cafke mutum 6 da ake zargi da harbe wani jigon PDP
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Wasu barayi sun yi wa masu gida 'wulankanci' a ban-daki bayan sun kasa shiga cikin gidan su yi sata

Sune: Bright Wali mai shekaru 21, Blessing Ogbuagu mai shekaru 23, Chineme Wemeh mai shekaru 26, Stanley Levi mai shekaru 19, Nnamdi Emenike mai shekaru 35 da Sunday Bright mai shekaru 35.

Ya ce, wadanda ake zargin an cafkesu ne a lokuta daban-daban kuma sun bayyana cewa duk 'yan kungiyar sirri ta Iceland da suka addabi jama'a Alakahia da Choba da ke karamar hukumar Obio/Akpor ta jihar.

Daya daga cikin wadanda ake zargin, Bright Wali, ya bayyana cewa, shi ya jagoranci kungiyar zuwa gidan wanda ya mutu kuma suka harbeshi. Bayaninshi ne ya zamo jagora a kama sauran mutane biyar din da ake zargi da kisan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel