Alimikhena da wasu 'yan majalisar APC a jihar Edo sun yi nasara a kotun daukaka kara

Alimikhena da wasu 'yan majalisar APC a jihar Edo sun yi nasara a kotun daukaka kara

Wata kotun daukaka kara mai zamanta a Benin, ta tabbatar da hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe da ke Edo wacce ta jaddada nasarar Sanata Francis Alimikhena na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar sanata mai wakiltar Edo ta arewa.

Kotun daukaka karar ta kara da tabbatar da nasarar Dennis Idahosa na jam'iyyar APC, Jude Ise-Idehen na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben majalisar wakilai na yankin Egor/Ipoba Okha na tarayya.

Kazalika, kotun daukaka karar ta yi watsi da karar Patrick Idiake na jam'iyyar APC da ke kalubalantar hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe da ta jaddada nasarar Joe Edionwele na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Esan ta yamma, Esan ta tsakiya da Igueben ta tarayya.

DUBA WANNAN: Kujerar Sanata: PDP ta sake lallasa tsohon gwamnan APC a kotun daukaka kara

Abubakar Momoh, Omosede Igbinedion duk 'yan jam'iyyar PDP da Johnson Agbonayinma tare da Patrick Idiake duk 'yan jam'iyyar APC sun daukaka kara ne sakamakon rashin gamsuwa da hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe sakamakon zargin magudin zabe da aka yi, a don haka suke bukatar a maida nasarar garesu.

Kotun ta yi watsi da kararrakin sakamakon rashin makama da kuma shaidun da zasu tabbatar da ikirarinsu.

Yayin yanke hukuncin kotun a ranar Juma'a, kotun daukaka karar tayi watsi da duk kararrakin tare da jaddada hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel