Shekau ya sake fitar da sabon sakon murya, ya gargadi wani lauya a Borno

Shekau ya sake fitar da sabon sakon murya, ya gargadi wani lauya a Borno

Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, a ranar Juma'a ya sake fitar da sabon sakon murya inda ya yi barazanar kaiwa wani lauyan Najeriya mazaunin kasar Ingila, Audu Bulama Bukarti hari kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Mista Bukarti, kwararren mai nazari ne a Cibiyar Tony Blair Institue for Global Change da ke jagorantar wata tawagar masu bincike kan ayyukan kungiyoyin masu tsatsauran ra'ayi a Afirka musamman Boko Haram na tsawon shekaru 10.

Lauyan ya mayar da hankali ne wurin amfani da hujojji daga cikin litafan addinin musulunci wurin yaki da tsauraran ra'ayoyi kuma ya wallafa wata takarda mai taken "Cikakken bayani kan Boko Haram", inda ya yi fashin baki kan kungiyar ta Boko Haram kuma samar da hujojji da za a iya amfani da su don kawar da tsaurarran ra'ayoyin da kungiyar ke koyarwa.

DUBA WANNAN: Barazanar hari: 'Yan bindigan Zamfara sun firgita 'yan makaranta

A cikin sakon muryar na tsawon minti 5 da ya yi wa lakabi da 'Martanin Shekau zuwa ga azzalumi (Bulama Bukarti)', Shugaban 'yan ta'addan ya ce Mista Bukarti ya shiga uku kuma ba daga yanzu (Juma'a) sun saka kafar wanda daya.

Ya fara jawabinsa kamar haka: "Tsarki ya tabbata ga Allah da manzonsa (SAW). Bayan haka ina yi wa 'yan uwa musulmi na duniya gaisuwa irin ta musulunci Assalamu Alaykum wa Rahmatullah.

"Mai magana shine shugaban kungiyar Jama’atu Ahlis Sunnah lid Dawati wal Jihad [JAS] wanda da izinin Allah ya ke magana a safiyar Juma'a 4 ga watan Rabi’ul Awwal 1441 AH. Wasu sakonni suni iske mu kuma mun san wanda ke yi kuma ba zai yi nasara ba."

Bayan haka, Shekau ya ce wannan sakon gargadi ne ga Bulama Bukarti don ya tuba kan irin maganganun da ya ke fadi kan JAS da shugabanta na cewa ba musulunci su ke yi ba. Ya gargadi Bukarti cewa maganganun da ya ke yi zai zama masa fitina muddin bai tuba ba.

Ya cigaba da cewa suna addini ne irin yadda Annabi (SAW) da sahhabansa suka yi kuma za su cigaba da hakan har zuwa ranar da za su mutu. Ya ce wannan huduba ce kuma gargadi don su ba komi suke so ba ila amfani da Qurani da Hadisi a matsayin doka.

Daga karshe ya ce za su cigaba da bin sahhun sahabbai wurin yin jihadi kuma ya sanar da Bulama Bukarti cewa daga yau ya shiga uku a duniya kuma ba zai taba samun kwanciyar hankali ba har sai ya tuba ya dena maganganu da rubuce-rubuce da ya ke yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel