Jigo a jam'iyyar APC ya yi mummunan hadarin mota, ya sha da kyar

Jigo a jam'iyyar APC ya yi mummunan hadarin mota, ya sha da kyar

Wani jigo a jam'iyyar All Progressive Congress (APC) a jihar Benue, Farfesa Eugene Aliegba a ranar Juma'a ya sha kyar bayan mummunan hadarin mota da ya ritsa da shi.

Hadarin ya afku ne a tittin Lafia zuwa Makurdi kusa da kauyen Daudu a jihar Benue.

The Nation ta ruwaito cewa Aliegba ya baro garin Keffi ne da ke jihar Nasarawa yana hanyarsa ta zuwa jihar Benue domin hallartar jana'izar wani abokinsa na kut-da-kut.

Wani shaidan ganin ido, James Ornguga ya ce motar su Aliegba ta yi ta yin kudun bala sau da yawa hakan ya sa aka ciro shi a jigace ta gilashin gobar motar kirar Toyota SUV.

DUBA WANNAN: Kujerar Sanata: PDP ta sake lallasa tsohon gwamnan APC a kotun daukaka kara

A halin yanzu an kwantar da shi a wani asibiti a Makurdi inda ya ke karbar magani.

Farfesa Aliegba ya yi kwamishina kwamishina har sau uku a ma'aikatu daban-daban a lokacin Gwamna Gabriel Suswam.

Ya yi takarar gwamna sau biyu a karkashin jam'iyyar People’s Democratic Party ( PDP) kafin daga bisani ya shiga jam'iyyar All Progressive Congress (APC) yayin babban zaben 2019 kuma an nada shi mamba na kwamitin yakin neman zaben Jime-Ode.

Ya cigaba da kasancewa dan jam'iyyar APC ko bayan kayen da jam'iyyar ta sha a zaben 2019 a jihar ta Benue.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel