NDLEA ta kwace miyagun kwayoyi masu tarin yawa a Kano cikin kwanaki 60

NDLEA ta kwace miyagun kwayoyi masu tarin yawa a Kano cikin kwanaki 60

Hukumar yaki da ta'ammali da miyagun kwayoyi, NDLEA, a jihar Kano ta ce ta kama miyagun kwayoyi masu nauyin 856.078kg a jihar tsakanin watan Satumba zuwa Oktoba, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Ibrahim Abdul, shugaban hukumar ta jihar Kano, ya sanar da manema labarai a ranar Alhamis cewa, hukumar ta bankado wani wajen da ake hada codeine ba bisa ka'ida ba a jihar.

Ya ce, "Mun kwace miyagun kwayoyin da suka hada da hodar ibilis, wiwi da sauran miyagun kwayoyi masu jimillar nauyin 856.078kg."

DUBA WANNAN: Barazanar hari: 'Yan bindigan Zamfara sun firgita 'yan makaranta

Kamar yadda yace, wannan ya nuna raguwa ba kadan ba na miyagun kwayoyi da safararsu a jihar. Ya kara da cewa, hukumar ta bankado wani dakin hada miyagun kwayoyi a yayin yaki da amfani dasu a jihar.

Abdul ya bayyana cewa, kididdigar ta nuna raguwa a ta'ammali da miyagun kwayoyin inda ya kai jihar Kano a matsayi na shida. A kwanakin baya kuwa jihar itace ta 3 a matakin.

Ya kara da cewa, a cikin lokacin kuwa, an bankado akalla waje 30 a cikin tsakar birnin Kano da wajenta inda ake siyarda kwayoyin.

Shugaban ya ce, an tura 17 daga ciki zuwa kotu, wanda hakan ya kai shari'u 89 a gaban kotun da ke jiran hukunci. An yankewa 6 hukuncin da ya dace dasu.

"Hakazalika, a cikin lokacin, an mika mutane 7 wajen bada shawarwari inda aka sallamo 2. An mika masu ta'ammali da miyagun kwayoyin 57 don samun shawarwari." in ji shi.

Ya kara da cewa, hukumar ta samu nasarori da yawa ballantana wajen raguwar amfani da miyagun kwayoyin a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel