Zuwa daya: Jami’an EFCC sun nade shuwagabannin kananan hukumomi 16 a jahar Kwara

Zuwa daya: Jami’an EFCC sun nade shuwagabannin kananan hukumomi 16 a jahar Kwara

Jami’an hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta kama wasu tsofaffin shuwagabannin kananan hukumomin jahar Kwara su 16 a kan zarginsu da karkatar da zunzurutun kudi naira biliyan 4.

Rahoton jaridar Punch ta ruwaito tun bayan zuwan sabon gwamnan jahar Kwara, Abdulrahman Abdulrazak ne ya dakatar da wadannan shuwagabannin kananan hukumomi kan zarginsu da barnatar da N4bn da kuma kashi 10 na kudaden shigar jahar.

KU KARANTA: Mai dokar barci ya buge da gyangyadi: Mai hukunta mazinata ya sha bulala saboda ya yi zina

Zuwa daya: Jami’an EFCC sun nade shuwagabannin kananan hukumomi 16 a jahar Kwara

Zuwa daya: Jami’an EFCC sun nade shuwagabannin kananan hukumomi 16 a jahar Kwara
Source: Twitter

Majiyar Legit.ng ta ruwaito daga cikin tsofaffin ciyamomin da EFCC ta kama akwai; Risikat Opakunle, Saidu Yaru Musa, Umar Belle, Ayeni Dallas, Fatai Adeniyi Garba, Lah Abdulmumeen, Raliat Funmi Salau, Aminat Omodara, Muyiwa Oladipo, Oladipo Omole, Abdullahi Abubakar Bata, Saka Eleyele, Lateef Gbadamosi, Oni Adebayo Joseph, Omokanye Joshua Olatunji da Jibril Salihu.

Cikin sanarwar da kaakakin EFCC, Wilson Uwujaren ya fitar a ranar Juma’a, 1 ga watan Nuwamba ya bayyana cewa ciyamonin sun amshi bashi ne, inda daga bisani suka amince su raba ma kawunansu naira miliyan dari dari.

“A ranar 7 ga watan Feburairun 2018 ne Ciyamomin sika tafi bankin Sterling dake Ilorin inda suka nemi bashin naira biliyan 4 domin su biya bashin albashi da malaman firamari suke binsu, tare da ma’aikatan kananan hukumomi da kuma yan fanshon kananan hukumomi, amma basu bayyana zasu raba miliyan 100 ga kowannensu ba a cikin takardar neman bashin.

“Haka zalika Ciyamomin suna karkatar da kaso 10 na kudaden shigar kananan hukumominsu domin amfanin kashin kansu, wanda kai tsaye ake aikawa cikin asusun bankunansu. Dukkaninsu sun amsa cin N100m daga bashin, da kuma cin kashi 10 na kudaden karamar hukumarsu.” Inji shi.

Daga karshe kaakakin EFCC yace a yanzu haka tsofaffin ciyamomin suna rokon EFCC ta basu lokaci zasu biya wadannan kudade gaba daya, sai dai EFCC za ta cigaba da rikesu har karshen mako, sa’annan ta gurfanar dasu gaban kotu da zarar ta kammala gudanar bincike a kansu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel