Bidiyo: Dan sanda ya turo budurwa daga saman bene saboda ya ce ta sanya Hijabi a jikinta taki sakawa

Bidiyo: Dan sanda ya turo budurwa daga saman bene saboda ya ce ta sanya Hijabi a jikinta taki sakawa

- Wani bidiyo da yake ta yawo a shafukan sadarwa ya bayyana yadda wani dan sanda ya ture wata mata kasa saboda taki sanya hijabi

- Bayan haka kuma dan sandan ya naushi wani mutumi a haba a lokacin da yayi kokarin kai wa matar dauki

- A dokar kasar Iran dole ne mace ta rufe dukkanin gashin kanta kada ta bari wani namiji ya gani

Wani bidiyo da ya fara yawo a shafukan sadarwa ya nuna yadda wani dan sanda na kasar Iran ya turo wata matashiyar budurwa daga saman bene saboda taki amincewa ta sanya Hijabi.

A bidiyon wanda wani dan jarida mai suna Masih Alinejad ya wallafa, ya bayyana yadda budurwar ta shiga wani waje mai suna Shahr-e-Rey, inda wani dan sanda ya nemi ta tsaya taki tsaya ta cigaba da tafiyar ta.

Wannan abu da tayi ya harzuka dan sandan inda ya ture ta kasa sannan ya naushi wani mutumi a haba a lokacin da ya zo ya kawo mata dauki.

KU KARANTA: Jarumi Sallau na 'Dadin Kowa' ya aikawa da Adam A Zango budaddiyar wasika

A ka'idat dokar shari'ar musulunci ta kasar Iran, dole ne mace ta rufe gashin kanta kada maza su gani, sai dai kuma matan sun fara fito suna nuna rashin goyon bayansu akan wannan doka da aka sanya.

Ga dai bidiyon yadda lamarin ya kasance a kasa:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel