Kujerar Sanata: PDP ta sake lallasa tsohon gwamnan APC a kotun daukaka kara

Kujerar Sanata: PDP ta sake lallasa tsohon gwamnan APC a kotun daukaka kara

Tsohon gwamnan jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi a ranar Juma'a ya sake shan kaye a kotun daukaka kara inda ya ke kallubalantar nasarar sanata mai wakiltan mazabar Oyo ta kudu, Sanata Kola Balogun a zaben ranar 23 ga watan Fabrairun 2019 na Majalisar Tarayya.

Kotun daukaka karar da ke zaman ta a Ibadan ta sake jadada hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe na Majalisar Tarayya a jihar ta yi na yin fatali da karar da Sanata Abiola Ajimobi ya shigar ta kallubalantar nasarar Sanata Dakta Kola Balogun.

Jam'iyyar APC da Ajimobi sun garyaza kotun daukaka karar suna neman kotun ta soke nasarar Balogun na jam'iyyar PDP da Hukumar Zabe Mai zaman kanta (INEC) ta tabbatar masa a kan wasu dalilai da suka hada da rashin cancanta takarar da kuma cewa sakamakon da INEC ta fitar ba hallastace bane.

DUBA WANNAN: Shari'ar Buhari da Atiku: Tambuwal ya yi tsokaci kan hukuncin da kotun koli ta yanke

INEC ta sanar cewa dan takarar na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 105,720 inda ya kayar da abokin hammayarsa na jam'iyyar APC da ya samu kuri'u 92,217.

Lauyoyin masu daukaka da Cif Akin Olujinmi (SAN) ke jagoranta sun yi ikirarin cewa kotun sauraron karrarkin zaben ba ta yi bitan hujjojin da aka gabatar mata ba sosai kafin yanke hukunci. Lauyoyin wanda aka yi kara karkashin jagorancin Mista Olalekan Ojo (SAN) su kuma sun ce kotun sauraron karar zaben ta duba dukkan hujjojin da aka gabatar mata kafin yanke hukuncin.

Mai shari'a Haruna Samani da ya yanke hukunci a madadin sauran alkalan biyu ya ce sashi na 138 (1) (a) ta ce muddin INEC ta tabbatar cewa dan takara ya cancanta ya tsaya zabe maganar rashin cancanta bai taso ba.

A kan ikirarin cewa kotun zaben ta da bi diddigi kan hujojji da shaidan da aka gabatar mata ba, kotun daukaka karar ta ce dukkan shaidan da aka gabatar ba su cancanta su bayar da shaida a kotun ba. Ya ce su dukkansu jami'ai ne na ofishin kidiya ba jami'ai da suka gudanar da zabe ba. Ba su da wani kwakwarar hujja da za su fada wa kotun hakan yasa aka yi watsi da su.

A karshe mai shari'a Samani ya ce karar da aka shigar ba ta wata madogara saboda haka ya yi watsi da ita kuma ya tabbatar da hukuncin da kotun zaben ta yanke a baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel