Barazanar hari: 'Yan bindigan Zamfara sun firgita 'yan makaranta

Barazanar hari: 'Yan bindigan Zamfara sun firgita 'yan makaranta

Wani yanki na jihar Zamfara sun shiga cikin rudani a ranar Alhamis bayan da wasu tsageru suka bar wasika a wata sananniyar makarantar sakandire Inda suka bukaci shugaban makarantar da ya rufe makarantar ko su kasheshi.

Wasikar da aka rubuta da hausa, an mannata ne a kofar ofishin shugaban makarantar sakandire ta gwamnati da ke Jangebe a karamar hukumar Talata Mafara da ke jihar Zamfara.

An ja kunnen shugaban makarantar da ya rufe makarantar daga 1 ga watan Nuwamba zuwa sati biyu masu zuwa. An ja kunnenshi cewa, rashin biyayya ga umarnin zai jawo sanadin kona makarantar tare da kashe shugaban makarantar, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito

DUBA WANNAN: Wasu barayi sun yi wa masu gida 'wulankanci' a ban-daki bayan sun kasa shiga cikin gidan su yi sata

.Mazaunan yankin sun ce akwai yuwuwar "Yan bindiga" ne suka manna wasikar a kofar ofishin.

Wannan barazanar kuwa ta taka rawar gani wajen kawo tashin hankula don kuwa malamai da dalibai da yawa sun ki halartar makarantar a ranar Juma'a.

An turo sojoji yankin a ranar Alhamis kuma sun taimaka wajen kwantar da hankulan mutane.

A yayin da aka tuntubi mai magana da yawun Rundunar sojin Hadarin Daji a daren Alhamis, Oni Orisan, yace bashi da bayanin aukuwar lamarin amma zai bincika kuma zai tuntubi jaridar Premium Times.

A wani tunanin da mazaunan yankin wajen suka yi, sun zai iya yuwuwa masu garkuwa da mutane ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel