NDDC: Ka salami Akpabio daga majalisarka yanzun nan – Shugabannin APC ga Buhari

NDDC: Ka salami Akpabio daga majalisarka yanzun nan – Shugabannin APC ga Buhari

Biyo bayan kafa kwanitin wucin gadi na hukumar cigaban Niger Delta (NDDC), shugabannin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na jihohin, sun bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kori tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Akpabio wanda ya kasance ministan harkokin Niger Delta, ya fusata shugabannin jam’iyyar lokacin da ya kafa sabon kwamitin hukumar NDDC duk da nadin mukamai da shugaban kasar ya yi.

Legit.ng ta rahoto cewa fusatattun shugabannin a ranar Juma’a, 1 ga watan Nuwamba, sun bayyana matakin Akpabio a matsayin tozarci ga kasa, inda suka kara da cewa ya zama dole Shugaban kasar ya dakatar dashi ba tare da bata lokaci ba.

A wani jawabi dauke da sa hannun shugabansu da sakatarensu, Ali Bukar Dolari da Ben Nwoye, sun bayyana Akpabio a matsayin mai hana ruwa gudu wajen cigaban gwamnatin Buhari.

KU KARANTA KUMA: Hukuncin kotun koli: Jigon APC Okechukwu ya yaba ma Atiku, ya taya Buhari murna

A cewarsa, ministan na da ra’ayin kansa na son kange hukumar NDDC a matsayin na bangare guda inda yake jagoranci a matsayin minista.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel