Zaben Bayelsa: PDP na kera katunan zabe na bogi gabannin zaben – Jigon APC ya yi zargi

Zaben Bayelsa: PDP na kera katunan zabe na bogi gabannin zaben – Jigon APC ya yi zargi

Mataimakin babban sakataren jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Mista Yekini Nabena ya yi zargin cewa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta fara kera katunan zabe na bogi gabannin zaben gwamnan jihar Bayelsa.

Mataimakin kakakin na APC ya yi zargin ne a cikin wani jawabi da aka aike wa manema labarai a ranar Juma’a, 1 ga watan Nuwamba.

A cewarsa, jam’iyyar PDP reshen Bayelsa ta sanya wa katin zaben na bogi suna "Biafra Card".

Ya bayyana cewa katunan tantance masu zabe 22 kacal hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta yi nasarar kwatowa cikin 69 da yan bangan siyasa suka sace a lokacin zaben Shugaban kasa da na majalisar dokoki na 2019 a jihar.

Jigon na APC wanda ya kasance haifaffen Bayelsa ya kuma yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari akan ya sanya baki a cikin lamarin, koda dai ya bukaci masu zabe a jihar da su yi adawa da wannan makirci da ake shirin yi.

KU KARANTA KUMA: Kotun daukaka kara ta soke sallamar dan majalisan PDP a Osun

Ya kuma yi kira ga hukumar INEC da su tashi tsaye akan lamarin sannan su tabbatar da ba a yi amfani da katin zabe na bogi ba a lokacin zaben.

A baya dai Nabena ya zargi PDP da razana ma’aikatan INEC a jihar gabannin zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel